Babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui a arewa maso yammacin kasar a jiya Laraba.
Xi ya ziyarci wata unguwar al’umma a birnin Yinchuan, babban birnin jihar, domin ganewa idanunsa yadda rassan jam’iyyar a matakin farko suke gudanar da ayyukansu. Ya kuma ga irin ayyukan da ake gudanarwa a unguwar wajen saukaka rayuwar jama’a da inganta mu’amala tsakanin al’ummar kabilu daban-daban.
- Kotu Ta Rushe Dokar Da Ta Tsige Aminu Ado Bayero A Matsayin Sarkin Kano
- Nijeriya Ta Koma Matsayi Na 38 A Cikin Sabon Jadawalin FIFA
Bugu da kari, yayin rangadin da ya kai lardin Qinghai daga ranar Talata zuwa Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin ci gaba da kokarin inganta kare muhallin tuddan Qinghai-Xizang,
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na JKS kuma shugaban hukumar koli ta soji, ya kuma yi kira ga lardin da ya inganta samar da ci gaba mai inganci. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)