Yankunan arewacin kasar Sin sun shiga yanayin sanyi a watan Nuwanba, don haka shugaban kasar Xi Jinping ya ziyarci wasu kauyukan birnin Beijing da lardin Hebei wadanda suka taba gamuwa da bala’in ambaliyar ruwa watanni uku da suka gabata a jiya Jumma’a 10 ga wannan wata, domin yin rangadin aikin duba ayyukan sake gina wuraren, tare kuma da kula da rayuwar manoman kauyukan a yanayin sanyi.
Yayin ziyararsa, shugaba Xi ya je gonaki don duba hatsin da aka shuka, saboda aikin gona muhimmin aiki ne daga cikin ayyukan sake gina wuraren da bala’in ya rutsa da su, inda ya yi nuni da cewa, girbin hatsi yana shafar kudin shigar manoma, haka kuma yana da nasaba da aikin samar da isasshen abinci na kasar. Ban da haka, shugaba Xi ya shiga gidajen manoma don aikin dumama dakunansu, kuma ya jaddada cewa, ya zama wajibi a tabbatar da aikin a kowanen dakin manoman. Haka zalika, shugaba Xi ya je kasuwanni don duba yanayin kasuwancin da suke ciki bayan bala’in, daga baya ya ba da umurni ga kananan gwamnatoci da su dauki matakai daban daban domin samar da tallafi ga al’umma da kamfanoni da ‘yan kasuwa da suke bukata, ta yadda za su gudanar da harkokinsu lami lafiya. (Mai fassara: Jamila)