Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban biki a birnin Lhasa, babban birnin yankin Xizang mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar yankin.
Bikin wanda zai samu halartar Xi, babban sakataren kwamitin kolinJKS, kuma shugaban kwamitin koli na soja, ana sa ran zai fara da karfe 10 na safiyar gobe Alhamis, kuma za a watsa shi kai-tsaye ta gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin da kuma kafar sadarwa ta Xinhuanet.
Kazalika, bayan isa birnin Lhasa na Xizang da maraicen yau, Xi ya karbi bakuncin wakilai daga sassa daban-daban na yankin, tare da mika gaisuwa da fatan alheri ga ‘ya’yan dukkan kabilun yankin Tibet, tare da bayyana fatan dukkansu za su ci gaba da hada karfi da karfe tare da yin aiki tare wajen rubuta wani sabon babi na kaifin basira game da hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin a yanki mai dusar kankara (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp