Farfajiyar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da ke arewa maso yammacin kasar Sin ya cika da ruguntsumin shagulgula na murnar cikarsa shekaru 70 da kafuwa tun daga farkon makon nan.
Yadda jama’ar yankin suka fito kawai da kwarkwata don yi wa Shugaba Xi Jinping lale marhabin da zuwa halartar gagarumin biki ya bayyana yanayi na farin ciki da kwanciyar hankali da suke ciki. Yankin ya samu sauye-sauye tun daga kafuwarsa a shekarar 1955, musamman ta fuskar aikin gona.
Baya ga raya al’adu, Xinjiang ya bude wani sabon babi na sauyin tattalin arziki, da fasaha, da aikin gona. A baya, ya yi kaurin suna a bangaren kwararowar hamada da sauran tarkace, amma a yau ya kasance abin misali a fagen samar da albarkatu, inda hakan ya ba shi damar zama ginshikin zamanantar da aikin gona a kasar Sin.
An yi nasarar habaka fiye da rabin daukacin fadin kasar noman yankin (kimanin hekta miliyan 3) zuwa filin noma mai inganci. Dimbin jarin da aka zuba a bangaren ayyukan ban ruwa, da kayan noma na zamani, da sauran ayyuka masu dorewa sun habaka ci gaban Xinjiang. A halin yanzu, auduga, tumatur, da tsirrai suna ci gaba da bunkasa a wuraren da a baya yashi ne kawai a malale.
Katafaren lambun aikin gona na fasahar zamani na Xinjiang ya nuna fasahar kirkira ta kasar Sin, inda ake amfani da fasahohin zamani irin su kirkirarriyar basira ta AI da karfin sadarwar 5G wajen kawo juyin-juya-halin noma. Nau’o’in amfanin gonar da a baya ke kwashe kwanaki 70 kafin su nuna, a yanzu ana girbe su cikin kwanaki 18 zuwa 25 kacal. Yankin ya bullo da sabbin nau’ikan amfanin gona sama da 2,000, tare da samun nasarorin binciken kimiyya sama da 100 da tuni aka fara amfani da su. Yankin na Xinjiang ne yake da kusan rabin adadin kamfanonin noman auduga na kasar Sin kuma ana fitar da audugarsa zuwa yankin tsakiyar Asiya, da Australia, da kuma Masar.
A yau, jihar Xinjiang tana bikin cika shekaru 70 da kafuwa cikin alfahari da kuma kyakkyawar manufa. Sauye-sauyen aikin gona a yankin suna nuna juriyar mutanensa da karfin hangen nesa yayin da karfin tattalin arzikinsa ya zuwa tsakiyar 2025, ya kai kudin Sin fiye da yuan tiriliyan 9.84 (kwatankwacin dala tiriliyan 1.35), bisa samun ci gaba da kaso 5.7 a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp