A rubu’i uku na farkon shekarar nan ta 2025, jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai ta kasar Sin, ta janyo karin jari daga wajen yankin, da ya kai kudin Sin yuan biliyan 847.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 119.5, adadin da ya karu da kaso 18.2 bisa dari a mizanin shekara-shakara.
Rahotanni daga ofishin lura da hada-hadar cinikayya na jihar, sun nuna cewa, jimillar adadin ayyukan zuba jari 4,006 ne aka aiwatar a jihar cikin wa’adin na watanni tara. Kazalika, wadannan ayyuka sun shafi sassan kyautata amfani da makamashin kwal, da samarwa, da sarrafa albarkatun danyen mai da iskar gas.
Ofishin ya kuma ce, akwai kudade da yawansu ya kai kusan yuan biliyan 566.8, da jihar ta Xinjiang ta samu daga larduna ko birane 19 na kasar, masu samar da tallafin hadin gwiwar bunkasa yankin, wanda ya kai kaso 66.9 bisa dari na jimillar tallafin da jihar ta samu. Kazalika, birnin Beijing, da lardunan Zhejiang da Guangdong, na kan gaba wajen samarwa jihar ta Xinjiang gudunmawa.
Tun daga shekarar 2012, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta ware kudaden da suka haura yuan biliyan 200, karkashin tsarin tallafi na hadin gwiwar sassa biyu ga jihar ta Xinjiang, wanda hakan ya taimakawa jihar wajen hawa turbar samun ci gaba mai inganci. (Saminu Alhassan)