Yau aka cika shekara guda da fara yakin Gaza, inda a ranar 7 ga Oktoba, 2023 mayakan Hamas sun kai hari mafi muni a Isra’ila.
A wannan rana mai tsanani, daruruwan mayakan Hamas sun kutsa kai cikin Isra’ila. Harin da ba a taba ganin irinsa ba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,205, akasarinsu fararen hula ne, a cewar wasu alkaluman jami’an Isra’ila na AFP.
- Shugabannin Tsaro Sun Gaza, Ya Kamata Gwamnati Ta Sake Lale – Farfesa Lugga
- Nazari Kan Gazawar Tsofaffin Ministocin Noma 52 Da Suka Shude A Nijeriya
Wannan adadin ya hada da mutanen da aka yi garkuwa da su daga baya suka mutu ko kuma aka kashe su a garkuwa da su a zirin Gaza.
Hamas ta yi garkuwa da mutane 251 zuwa Gaza, wasu a matsayin gawarwaki. Shekara guda bayan haka, har yanzu ana tsare da wasu 64, yayin da 117 aka sake su, sannan 70 aka tabbatar sun mutu.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ruguza kungiyar Hamas da Tarayyar Turai da Amurka suka sanya a jerin sunayen ‘yan ta’adda.
Yayin da take shan alwashin murkushe Hamas tare da mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su gida, Isra’ila ta kaddamar da yakin soji a zirin Gaza daga kasa, ruwa da kuma sarari subhana.
Isra’ila ta fara kai hare-hare a zirin Gaza tare da kara tsaurara matakan killace yankin. A ranar 13 ga Oktoba, inda ta gaya wa fararen hula a Arewacin Gaza su matsa zuwa Kudu.
Daga baya Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kusan dukkanin mutanen Gaza miliyan 2.4 sun rasa matsugunansu.
A anar 27 ga Oktoba, Isra’ila ta kai farmaki ta kasa.
A cewar bayanan da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta Hamas ta bayar a ranar Lahadi, yakin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla 41,870, yawancinsu fararen hula ne.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana wadannan alkaluma a matsayin abin dogaro.
Girman barnar da aka yi daga yakin mafi muni a tarihin Gaza ya sanya hanyar samun saukin rayuwa mai wahalar tunani, musamman ga mutanen da suka rigaya suka yi hasarar gidajensu a rikicin baya.
Hamas dai na rike da yankin Gaza tare da tafiyar da cibiyoyinta da hannu daya tun a shekara ta 2007, bayan da ta lashe zaben ‘yan majalisar dokoki shekara guda da ta gabata tare da murkushe abokan hamayyarta Fatah a fadan tituna.
A yanzu, yawancin cibiyoyin Gaza ko dai rushe su ko kuma sun lalace.
Isra’ila na zargin Hamas da amfani da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya da sauran kayayyakin more rayuwa na farar hula wajen gudanar da ayyukan Hamas, da’awar da Hamas din ta musanta.
Yakin bai bar wani yanki na Gaza da ya tsira daga harin bam ba: makarantu sun zama matsuguni ga ‘yan gudun hijira, an kai hari wuraren kiwon lafiya.
Dubban daruruwan yara ne ba sa zuwa makaranta a kusan shekara guda, yayin da jami’o’i da na’urorin samar da wutar lantarki da tashoshin ruwa da kuma ofisoshin ‘yansanda suka daina aiki.
A tsakiyar shekara ta 2024, tattalin arzikin Gaza ya ragu zuwa “kasa da kashi daya bisa shida na matakinta na 2022,” in ji wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya ce zai dauki “shekaru goma kafin a dawo da Gaza” zuwa yadda take a baya kafin 7 ga Oktoba.
Wannan rushewa ta haifar da rashin jin dadi a tsakanin mutane miliyan 2.4 na Gaza, kashi biyu cikin uku sun zama matalauta kafin yakin, a cewar Mukhaimer Abu Saada, wani mai binciken siyasa a jami’ar Al-Azhar a Alkahira.
A ranar 24 ga Nuwamba, an shafe mako guda ana tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas. Kungiyar Hamas ta saki Isra’ilawa 80 da ta yi garkuwa da su a matsayin mayar da martani ga Falasdinawa 240 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.
Haka kuma an kubutar da wasu mutum 25 da aka yi garkuwa da su, galibinsu ma’aikatan gona ne na Kasar Thailand. Isra’ila ta ba da karin taimako zuwa Gaza ta Masar, amma yanayin jin kai a can ya kasance mai muni. Lokacin da fada ya sake barkewa, Isra’ila ta fadada ayyukanta zuwa Kudancin Gaza.
A ranar 7 ga watan Mayu ne sojojin Isra’ila suka kaddamar da farmaki ta kasa a Rafah, a Kudancin Gaza, inda akasarin mutanen yankin suka nemi mafaka.
Ta kwace iko da kan iyakar kasar da Masar, tare da toshe wata muhimmiyar hanyar shigar da kayan agaji, sannan ta kai hari a wuraren da ba a amince da su ba da suka hada da sansanonin tantuna da makarantu da ke ba da mafaka ga ‘yan gudun hijira.
Dubban mutane sun yi zanga-zanga a duniya
Dubun dubatar masu mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a biranen duniya a karshen mako inda suke kira da a tsagaita wuta a Gaza da Lebanon yayin da yakin Falasdinawa ya shiga cika shekara guda.
A Birnin Washington, masu zanga-zanga fiye da dubu daya ne suka gudanar da zanga-zanga a wajen fadar White House, inda suka bukaci Amurka, babbar mai samar da sojan Isra’ila, ta daina ba da makamai da taimako ga Isra’ila.
Dubban magoya bayan Falasdinawa ne kuma suka hallara a biranen Turai da Afirka da Ostireliya da kuma Amurka domin neman kawo karshen rikicin.
Ana sa ran za a gudanar da taron tunawa da ranar tunawa da harin da Hamas ta kai kan Isra’ila.
Yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare ta kasa a kasar Labanon tare da shan alwashin mayar da martani kan harba makami mai linzami da Iran ta harba a cikin wannan mako, ana fargabar rikicin na iya rikidewa zuwa wani yaki.
Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Birnin Rome da ya janyo ta koma tashin hankali, yayin da dimbin matasa masu zanga-zangar suka yi ta jifa da kwalabe da harbe-harbe a kan ‘yan sanda, wadanda suka mayar da martani da hayaki mai sa hawaye da kuma na ruwa.
A Berlin, ‘yan sanda sun ce sun tsare mutane 26 da suka yi ihun zagi a wani taron tunawa da Isra’ila da ya samu halartar kusan mutane 650.
A halin da ake ciki kuma, zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ta tara masu zanga-zanga sama da 1,000 a Babban Birnin Jamus, in ji ‘yan sanda.
A taron “Tattaunawar Kasa don Falasdnu” da aka yi a Landan, an hada da wake-wake na “dakatar da farar hula” da ihun “hannu daga Lebanon”.
A Dublin, daruruwan mutane ne suka fito kan tituna, suna daga tutocin Falasdinawa suna rera cewa: “A tsagaita wuta yanzu!”.
A Faransa dubban mutane ne suka yi jerin gwano a biranen Paris, Lyon, Toulouse, Bordeaud da Strasbourg domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa.
Kimanin mutum 5,000 ne suka shiga zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Madrid, suna nuna alamun da ke dauke da sakonni kamar “Kauracewa Isra’ila”. Kamfanin Dillancin Labarai na Keystone-ATS ya bayar da rahoton cewa, zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a Birnin Basel na kasar Switzerland, ta jawo ce-ce-ku-ce.
Daruruwan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa ne kuma suka yi maci a ofishin jakadancin Isra’ila da ke Athens.
A Cape Town a Afirka ta Kudu, daruruwan sun yi tattaki zuwa majalisar dokoki, suna rera waka: “Isra’ila kasa ce mai nuna wariyar launin fata” da kuma “Dukkanmu Falasdinawa ne.” Sun gabatar da koke ga Majalisar Dinkin Duniya na neman kawo karshen “kisan kare dangi” na Falasdinawa.
A Ostiraliya, dubban masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ne suka yi dafifi a kan titunan Sydney da sauran manyan biranen Australiya, suna rike da allunan da aka rubuta “Dakatar da Isra’ila”.
An shirya wasu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a karshen mako da kuma ranar Litinin a biranen New York, Sydney, Buenos Aires, Madrid, Manila, da Karachi.
An kuma shirya gudanar da bukukuwan tunawa da wadanda harin na ranar 7 ga watan Oktoba ya rutsa da su a kasashen duniya, ciki har da bukukuwa a London, da Washington, da Paris da kuma Geneba.
A ranar Litinin ne za a gudanar da bikin cika shekaru a hukumance a Birnin Kudus.
Shugaban Isra’ila Isaac Herzog zai jagoranci taron tunawa da ‘yan ta’adda a Sderot, daya daga cikin garuruwan da aka fi fama da hare-haren da mayakan Falasdinawan ke kai wa.