• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Dace Amurka Ta Dauki Hakikanin Matakai Domin Karfafa Hadin Gwiwa Da Sin

by CMG Hausa
2 years ago
Amurka

Jiya ne, sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen ta kammala ziyararta ta kwanaki hudu a kasar Sin. Yayin shawarwarin da sassan biyu suka yi lokacin ziyararta, Sin da Amurka sun nuna aniyarsu ta kara karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakaninsu.

Jami’an kasar Sin sun jaddada cewa, matakin da bangaren Amurka ya dauka ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa zai kawo cikas ga huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, A nata jawabin, Yellen ta sake bayyana cewa, kasarta ba ta son rabuwa da kasar Sin a bangaren tattalin arziki, kuma ta yi alkawari cewa, za ta yi kokarin kyautata hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasarta da kasar Sin domin samun moriya tare.

  • Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Dandalin Samun Ci Gaba Tare Na Kasa Da Kasa

Yellen, ita ce babbar jami’ar gwamnatin Amurka ta biyu da ta kawo ziyara kasar Sin a cikin wata guda. Kafin wannan, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ziyarci kasar Sin. Bisa bayanan da bangarorin biyu suka fitar, ziyarar Yellen a wannan karon ta baiwa kasashen Sin da Amurka damar kara fahimtar damuwar juna, kana bangarorin biyu sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da tattaunawa.

Amma an lura cewa, Yellen tana ci gaba da bayyana wasu manufofin Amurka da ba su dace ba bisa fakewa da batun tsaron kasa, inda ta sanar da cewa, za ta tsara wani tsarin tattalin arziki mai adalci. Bangaren kasar Sin shi ma ya nuna damuwa kan takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Sin. Masu sharhi sun yi nuni da cewa, har yanzu akwai bambance-bambance a tsakanin Sin da Amurka ta fuskar inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, musamman ma cewa har yanzu ya dace Amurka ta kara kokari.

Bayan Yellen ta koma kasarta, ana sa ran gwamnatin Amurka za ta dauki hakikanin matakai domin ciyar da huldarta da kasar Sin gaba yadda ya kamata. (Mai fassara: Jamila)

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji

Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.