• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Dace Sin Da Afirka Su Bunkasa Hadin Gwiwar Cin Gajiya Daga Fasahohin Amfani Da Makamashi Maras Illa Ga Muhalli

by CMG Hausa
3 years ago
Afirka

Yayin da hankulan duniya ke kara karkata ga yadda za ta karke a taron COP27, na bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, masharhanta da dama na ganin taron babbar dama ce ga daukacin masu ruwa da tsaki, ta su hada karfi da karfe wajen lalubo dabarun gaggauwa na shawo kan kalubalen sauyin yanayi, ciki kuwa har da dabarun rage radadin sauyin yanayin, da gano fasahohin jurewa da dorewar rayuwa tare da kalubalen, da rage asarar da sauyin yanayin ka iya haifarwa, da ma batun samar da kudaden gudanar da wadannan ayyuka.

Tuni dai aka yi imanin cewa, nahiyar Afirka na cikin yankunan duniya dake fitar da mafi karancin sinadarai, da iska mai gurbata muhalli a duniya, amma a hannu guda, nahiyar na sahun gaba wajen dandana kuda daga mummunan tasirin sauyin yanayi.

  • CMG Ya Shirya Bikin Musammam Game Da “Sabon Tafarki Na Sin Da Duniya” A Afirka

Masharhanta na ganin duba da yadda kasar Sin ke kan gaba, wajen cin gajiya daga fasahohin dakile sauyin yanayi, musamman fannin bunkasa amfani da nauoin makamashi marasa gurbata muhalli, da wadanda ake iya sabuntawa. Kuma kasar ta jima da kasancewa abokiyar tafiya ga kasashen Afirka a dukkanin fannonin ci gaba, yanzu lokaci yayi da kasashen na Afirka za su fadada koyi daga kasar Sin a wannan fanni.

A cewar Frederick Mutesa, wani kwararre a fannin ilimin samar da ci gaba dan kasar Zambia, kasar Sin ta nunawa duniya kwazon ta a fili wajen bunkasa ci gaba mai dorewa, da raya manufofi na dakile kalubale da matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa. Don haka lokaci ya yi da kasashen Afirka za su gaggauta yin hadin gwiwa da Sin, ta yadda za su yi koyi, da kuma cin gajiyar kwarewar Sin a wannan fanni.

Ko shakka ba bu wannan shawara ce mai kyau, domin kuwa akasarin kasashen nahiyar Afirka na da albarkatu musamman na hasken rana, yayin da a daya bangaren kasar Sin ke da kwarewa, da fasahohin bunkasa samar da makamashi ta hasken rana, wanda hakan ke nuna cewa, idan har sassan biyu sun yi hadin gwiwa, tabbas za a ci babbar gajiya daga makamashi maras gurbata muhalli.

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Baya ga fannin raba fasahohi da kasashen Afirka, fannin samar da kudaden dakile tasirin sauyin yanayi, shi ma muhimmin bangare ne da kasashen Afirka za su iya cin gajiya daga Sin, kasancewar dama akwai kyakkyawar dangantaka, da cudanya tsakanin kasashen Afirka da Sin karkashin dandalin FOCAC na bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma irin tallafi na samar da manyan ababen more rayuwa da kasashen Afirka ke samu daga Sin, karkashin manufofin samar da ci gaba na shawarar ziri daya da hanya daya.

Duk wadannan dalilai, na kara nuna muhimmancin aza kyakkyawan mafari, na ingiza hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin kare muhalli, da bunkasa cin gajiya daga nauoin makamashi da ake iya sabuntawa.(Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
Daga Birnin Sin

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
Next Post
Hedikwatar Tsaro Ta Ayyana Neman ‘Yan Ta’adda 19 Ruwa A Jallo, Ta Sa Ladar Miliyan 5 Kan Kowanne

Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta’adda 29 Da Cafke Masu Taimaka Musu 10 Da Naira Miliyan 15

LABARAI MASU NASABA

2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

November 3, 2025
Likitoci

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

November 3, 2025
Kano

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.