A cikin makon da ya gabata, an gudanar da babban taron MDD na 80 a hedkwatar majalisar dake birnin New York. Wasu da suka bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da makomar MDD da ta kai shekaru 80, duba da yadda duniyar ke fuskantar rikice-rikice da sauye-sauye. Duk da hakan, bangarori da yawa sun bayyana goyon bayansu ga majalisar.
A zahiri, bayan muhawarar “Ina MDD ta nufa a nan gaba?”, akwai ra’ayoyi biyu da suka saba da juna kan tsarin shugabancin duniya. Na daya shi ne rikon daidaiton ‘yancin kai, mutunta juna, nacewa ga ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori a duniya da bin dokokin kasa da kasa, da kuma hadin kai da cin moriya tare. Yayin da ra’ayi na biyu ya karkata ga kasashe masu dogara ga karfi da fifita kansu, da sanya kansu a gaban komai da bin ra’ayin bangaranci. Tabbas, ra’ayi na farko yana wakiltar al’adar zamani da adalcin duniya. Dole ne mu bi wannan ra’ayi, mu nace ga ka’idojin MDD duk da kalubalen da ake fuskanta, mu yiwa majalisar gyare-gyare bisa wannan daidaitaccen ra’ayi, ta yadda majalisar za ta sauke nauyin dake wuyanta.
A matsayinta na daya daga cikin kasashe mambobin MDD na farko tun kafuwarta, Sin ta kasance mai goyon bayan kokarin majalisar wajen daidaita harkokin duniya. A taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai da aka yi a birnin Tianjin, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara gabatar da shawarar tsarin shugabancin duniya, wanda ya nuna madaidaiciyar hanyar gina tsarin shugabancin duniya mai adalci. Babban sakataren MDD António Guterres, ya yi imanin cewa, shawarar da Xi ya gabatar tana da cikakkiyar ma’ana, kuma manufofinta sun yi daidai da ruhi da gwagwarmayar MDD, inda ta mayar da martani mai karfi ga bukatun duniya na gyara tsarin shugabancin duniya.
Muna fatan samun ci gaba mai kyau nan gaba ta hanyar waiwayi tarihi. A wannan muhimmin lokaci na cika shekaru 80 da kafa MDD, Sin za ta ci gaba da rike manufofi da ka’idojin majalisar, tare da sauran kasashe, don gina duniya mai jituwa da zaman lafiya.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp