Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Yayin taron, wani dan jarida ya yi tambayar ko Sin da Amurka za su yi tattaunawa game da batun harajin kwastam.
- An Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Bayan Kwana 9 Da Aurensu A Kano
- Saudiyya Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Aikin Hajji Babu Takardun Izini
Lin Jian ya bayyana cewa, Amurka ce ta kaddamar da yakin harajin kwastam din, kuma matsayin bangaren Sin a bayyane yake, wato idan Amurka na so yaki, Sin za ta yi yaki, idan kuma Amurka na so tattaunawa, to Sin tana maraba da hakan. Kwanan nan Amurka ta sha bayyana fatanta na yin tattaunawa da Sin. Idan da gaske Amurka na son warware batun ta hanyar tattaunawa, kamata ya yi ta daina yin barazana da matsa lamba, ta shiga tattaunawa da Sin bisa daidaito, mutunta.
Game da dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar EU, Lin Jian ya ce, darussa da aka samu yayin bunkasa dangantakar Sin da EU cikin shekaru 50 da suka gabata, su ne mutunta juna da kuma kiyaye bambanci dake tsakaninsu. Sin da kasashen Turai suna da bambanci a fannonin tarihi, al’adu, da tsare-tsaren tafiyar da harkokin kasa, amma idan bangarorin biyu sun mutunta hanyar samun ci gaba da tsarin zamantakewa da jama’arsu suka zaba, bangarorin biyu za su iya samun ci gaba tare da samun moriyar juna da samun nasara yayin yin koyi da yin hadin gwiwa tsakanin juna. Ya kuma ce, Sin da majalisar Turai sun yanke shawarar soke takunkumin da aka sanya a kan mu’amalar juna a lokaci guda.
Bugu da kari, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin ya nuna godiya da taya kasar Togo murna nasarar kammala mika mulki a siyasance da kuma zaben sabon shugaban kasar da shugaban majalisar ministocinta na farko.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp