Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau cewa, ya kamata kasar Amurka ta dakatar da mamaye yankuna mallakar kasar Cuba ba bisa doka ba, da gaggauta rufe gidan kurkuku na Guantanamo, da kuma janye kasar Cuba daga jerin sunayen kasashe masu goyon bayan ta’addanci.
Lin Jian ya bayyana cewa, gidan kurkuku na Guantanamo wuri ne dake haifar da bakin ciki ga kasar Cuba, kana shi ne shaidar dake nuna cewa Amurka tana tsoma baki cikin harkokin kasar Cuba cikin fiye da karni daya. Ya ce kasar Amurka ta yi garkuwa da mutane a gidan kurkuku na Guantanamo, kana ta shigar da kasar Cuba cikin jerin kasashe masu goyon bayan ta’addanci, yana mai cewa, duniya ta san irin ma’auni biyu da kasar Amurka take amfani da shi. Ya ce kasar Sin tana goyon bayan kasar Cuba ta tabbatar da ikon mallakar yankunanta da kare mutuncin kasar, kuma tana adawa da Amurka ta rika tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Cuba. (Zainab Zhang)