A baya bayan nan ne aka bude ofishin jakadancin Amurka a tsibirin Solomon, wanda ya kasance rufe tsawon shekaru 30. Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wata sanarwa tana cewa, za ta tura jami’an diflomasiyya zuwa yankin na Fasifik. Wannan abu ne mai kyau, idan har Amurka za ta yi amfani da damar wajen taimakawa kasashen tsibiran Pasifik da zuciya daya da kuma hada gwiwa da kasa da kasa wajen inganta ci gabansu. Sai dai, wannan ya saba da tunanin galibin kafafen yada labarai na kasashen yammacin duniya, inda suke ganin hakan wani yunkuri ne na dakile kasar Sin da gaggauta aiwatar da shirinta a yankin Asiya da Pasifik. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp