A yayin da makarantun firamare da sakandare a fadin jihohi 36 na Nijeriya za su koma makaranta a wannan makon bayan dogon hutu, shugaban kungiyar iyayen yara na Nijeriya, (PTAN), Alhaji Haruna Danjuma ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su samar da isasshen tsaro a duk makarantu, domin kauce wa kalubalen tsaro.
A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna, ya jaddada muhimmancin samar da isassun jami’an tsaro a harabar makarantar domin dakile ayyukan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ke dagula tarbiyar yara.
- Me Ya Sa Ba A Fara Shekarar Hijirah Da Ranar Badar Ko Ranar Cikar Wahayi Ba? (II)
- Yarima Charles Ya Zama Sabon Sarkin Ingila
Ya ce “Muna rokon daukacin jihohin Nijeriya 36 da gwamnatin tarayya da su taimaka mana da kare yaranmu ta hanyar samar da isassun jami’an tsaro a harabar makarantu.”
A cewarsa, cutar Karona har yanzu babbar barazana ce ga wanzuwar Dan’adam, don haka akwai bukatar samar da abin rufe fuska, tsabtace hannu, ilimantar da daliban kan nisantar jama’a.
Ya tunatar da gwamnatin Jihar Kebbi da gwamnatin tarayya da su kara kaimi wajen ganin an ceto daliban mata da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandare ta Yawuri.
A cewarsa, har yanzu ‘yan matan sakandaren Yawuri sun kwashe sama da kwanaki 450 a hannunsu kuma babu mai magana a kai.
Ya kara da cewa har ya zuwa yanzu akwai wasu daliban makaranta a hannan masu garkuwa.
Ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya na yaki da ta’addanci da suka hada da ‘yan fashi, ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma matsalolin rashin tsaro gaba daya da ke haifar da rashin zaman lafiya a kasar.