Ana daf da kaddamar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC karo na 31 a kasar Peru, muhimmin taron da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta.
A matsayin ta na muhimmin jigon tattalin arzikin yankin Asiya da Pacifik, kasar Sin ta jima tana taka rawar gani a hadin gwiwa da mambobin APEC. Daga kokarinta na yayata bukatar karfafa dunkulewar yankinta zuwa jaddada kirkire- kirkire, da yin komai a bude, da samar da ci gaba maras gurbata muhalli, manufofi da shawarwarin da Sin ke gabatarwa a yayin kwarya-kwaryar tarukan shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC da suka gabata, sun dace da bukatun ci gaban yankin, sun kuma samu yabo da goyon baya daga sassa daban daban.
Nacewa yin komai a bude da hadin gwiwa, sun zamo sirrin nasarar yankin Asiya da Pacifik, su ne kuma abun da ya dace su zama ginshikan kara bunkasa yankin Asiya da Pacifik a nan gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)