Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya bayyana a yau Alhamis cewa, har kullum kasar Sin na adawa da sanya takunkumi don kashin kai, da daukar matakai kan wasu kasashe bisa dokokin kasar Amurka, kuma kamata ya yi Sin da Amurka su dauki matakai bisa buri iri daya, a kokarin samar da kyakkyawan yanayi, da sharudda na yin hadin gwiwa a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.
Dangane da ra’ayin wasu jami’an Amurka, kan sanya takunkumi ga kayayyakin da kamfanonin kasar Sin suke sayarwa Amurka, Gao Feng ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta amince da matakin ba.
Kakakin ya kara da cewa, a kwanan baya, gwamnatin Amurka ta yi nazarci batun soke karin haraji da ta dora kan kayayyakin kasar Sin, lamarin da ya dace da muradun masana’antun Sin da Amurka, da muraddun Amurkawa masu sayayya, da ma muraddun kasashen duniya baki daya.
Ya ce kamata ya yi Sin da Amurka su dauki matakai bisa buri iri daya, a kokarin samar da kyakkyawan yanayi da sharudda na yin hadin gwiwa a tsakaninsu, ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da kara samarwa al’ummun kasashen 2 alherai. (Tasallah Yuan)