Wani dan shekara 17 mai suna Ade Segun a jihar Delta, ya fada hannun ‘yansanda a jihar bisa tsara sace kansa don ya karbar kudin fansa Naira miliyan 20 daga hannun iyayensa da ke zaune a garin Warri.Â
Kakakin rundunar ‘yansanda na jihar, DSP Bright Edafe, ya bayyana wa manema labarai hakan a garin Asaba, inda ya ce, rundunar ta kuma cafko abokan harkallarsa mutum biyu – Precious da Nonso.
Edafe ya ce, Segun a ranar 9 ga watan Mayun 2023, ya tsara sace kansa da hadin bakin wasu abokansa domin damfarar iyayensa Naira miliyan 20.
Ya ci gaba da cewa, Precious da Nonso sun kira iyayen Segun a wayar tarho inda suka bukaci a basu kudin fansa Naira miliyan 20 kafin su sako Segun.
Kakakin ya kara da cewa, iyayen Segun sun kai rahoton maganar a caji ofis din ‘yansanda da ke a Warri, inda caji ofis din ya yi amfani da wata ‘yarsanda da ta boye asalinta ta nuna cewa za ta biya su kudin fansar da suka bukata.
A cewarsa, bayan da wasu ‘yansanda suka yi shigar burtu suka isa inda abokan Segun suke, sai suka yi kwanton Bauna, inda Precious ya fito don amsar kudin sai ‘yansandan suka zagaye shi suka kuma kama shi.
Precious ya jagoranci ‘yansandan zuwa maboyar da Segun da Nonso suke, inda dukkanin su, suka amsa cewa, su ne suka tsara yin garkuwar don mallakar makudan kudaden.