Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce, ta cika hannu da wani ƙasurgumin mai fataucin miyagun ƙwayoyi da wasu mutum biyar da ta ke zargi da harƙallar saka miyagun ƙwayoyi a jakunkunan matafiya a filin jirgin saman Aminu Kano.
Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa, Femi Babafemi ya fitar.
- Adadin Cinikayyar Sin Da Kasashen Kungiyar SCO Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi
- Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama
Sanarwar ta ce, wani mai suna Mohammed Ali Abubakar mai shekara 55 da aka fi sani da Bello Karama da wasu mutum biyar ne suke harƙallar a filin jirgin, inda suke haɗa hannu da wasu ma’aikata wajen harƙallar.
Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara.
Da yake bayyana yadda aka bankaɗo harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani ba cikin masifa, ya ce ‘yan uwan wadanda aka kama ne a Saudiyya ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ’yan uwan su a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike.
“’Yan Nijeriya da aka kama a Saudiyya su ne: Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abulhamid Sadiq waɗanda suka hau jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940, wanda ya bar Kano a ranar 6 ga watan Agustan bana zuwa Jeddah, sai aka qara wasu jakunkuna da sunan su da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi.”
Ya ce, bayan mutanen sun je karvar jakunkunan su ne sai aka tsare su bisa zargin fataucin miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar.
“Binciken mu ya gano Ali Abubakar Mohammed wanda ake kira da Bello Karama ne ya kai jakunkunan a ranar 6 ga watan, wadda ita ce ranar da waɗanda ake zargin suka yi tafiya’.
”Amma sai shi (Ali Abubakar Mohammed) ya hau jirgin Egypt Air zuwa Saudiya, amma ya saka jakunkunan a jirgin Ethiopian tare da waɗanda suka hau.”
Femi ya ce wasu ma’aikatan kamfanin Skyway Aviation Handling Company ne suka shigar da jakunkunan da ke ɗauke da ƙwayoyin, sannan suka rubuta sunan waɗanda aka zarga ba tare da sanin su ba, wanda hakan ya sa hukumomi a Saudiyya suka tsare mutanen.
“Amma bayan bincike, mun tabbatar da cewa waɗanda ake zargi ba su da laifin komai, kawai gungun wau mutane ne suka shirya harƙallar a filin jirgin Aminu Kano.”
Hukumar ta ce, tuni mutum shida sun shiga hannu, sannan akwai huɗu da an riga an gabatar da su a kotu.
Waɗanda ya ce an gabatar a kotu su ne: Ali Abubakar Mohammed (Bello Karama) da Abdulbasit Adamu da Murtala Akande Olalekan da Celestina Emmanuel Yayock.
“Sun tabbatar da hannunsu a aukuwar lamarin, inda Ali ya tabbatar da zuwa jakunkunan. Celestina ta ce ita ta shigar da jakunkuna biyu a kan Naira 100,000, wani mai suna Jazuli Kabir ya ce shi ya shigar da jakunkuna biyu a kan Naira 100,000.”
Ya ce hukumar na aiki da hukumomin Saudiyya wajen wanke waɗanda ake zargi, “Shugaban mu zai tafi Saudiyya domin gabatar da sakamakon binciken da muka yi domin ganin an saki, tare da wanke Maryam Hussain Abdullahi da sauran mutanen guda biyu.”
Hukumar ta nanata cewa a shirye take ta ci gaba da yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar, inda ya ƙara da cewa “babu sani ba sabo” a aikinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp