‘Yansanda a jihar Nasarawa sun tabbatar da cewa, masu garkuwa, sun kama wani kwamishina a jihar Nasarawa mai suna Yakubu Lawal,kwamishinan yada labarai da al’adu da yawon shakatawa da gandun daji na jihar Nasarawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da wannan labarin a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Lafiya babban birnin jihar.
Kanar yadda jami’in ya ce, “Ranar Litinin da daddare. ‘yansandan da ke zagaya wa cikin gari, suna tafiya sai suka ji karar bindiga a yankin karamar hukumar Nassarawa-Eggon da ke babban birnin jihar.
Ya ce, sai ‘yansandan da ke Nassarawa-Eggon, suka shirya suka fito, suka tunkari inda ake wannan ruwan-wuta. Jin haka nan da nan kwamishinan ‘yansanda Adesina Soyemi, ya kara wa ‘yansandan karfi, inda suka samu karin karfin gwiwar fuskantar masu garkuwar.
“Bayan da ‘yansandan suka je inda masu garkuwan suke, sai suka samu garkuwar sun ranta a na kare sun kuma tafi da kwamishinan yada kabarai da al’adu da yawon shakatawa na jihar.
Jami’in hulda da jama’ar ya ce, kwamishinan na gabatar da nemi al’ummar jihar su bayar da gudummowa wajen ganin an kawo karshen ta’addanci da sace mutane a yi garkuwa da su, domin a karbi kudin fansa.