Ruwan da aka wanke shinkafa da shi ko aka tafasa shinkafa da shi ya kasance ana amfani da shi wurin gyaran gashi da fata kusan shekaru 1,000 da suka wuce a Kasar Japan.
A yau ruwan shinkafa na kara samun karbuwa a fannin gyaran jiki, domin yana gyara fata da sanya fata sheki da magance wasu matsolin fata.
Masu hada sabulai da maiyuka na amfani da shi, abin burgewa shi ne za ki iya hada ruwan shinkafa a gida cikin sauki.
Ruwan shinkafa yana tattare da wasu sinadarai da suke gyara fata
Yadda ake hada ruwan shinkafa
1- Tafasawa
Za’a samo shinkafa ko wace iri a wanke sannan a zuba ruwa a tukunya sai a zuba juye shinkafar a ciki a barshi ya tafasa, sannan a sauke a tsiyaye ruwan a barshi ya yi sanyi sai a zuba a gora.
Idan za’a yi amfani da shi sai a diba a sirka da ruwa za’a iya matsa lemun tsami a ciki sai a rika wanke fuska da shi kamar sau uku a sati.
2- Jikawa
Za’a samu shinkafa sai a zuba a roba a dauraye shi da farko, sai a nemi abu mai murfi a juye shinkafar a ciki sannan a zuba ruwa a rufe sai a barshi na awanni idan ruwan ya yi fari sai a tsiyaye ruwan cikin gora sai a rufe.