Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya. A yau shafin namu zai kawo muku yadda ake Awarar Zamani:
Abubuwan da ake bukata:
Waken soya, alam ko ruwan tsami, magi, shiri, tattasai ko attaruhu, tomator, albasa, kori:
Yadda za ki hada:
Da farko za ki samo waken soya sannan ki gyara shi ki jika ya kwana ki wanke shi a nika muki sai ki tace, sannan ki samu tukunya babba wadda za ta dauka sai ki zuba a ciki, sannan ki dora a wuta ki zuba magi da dan gishiri ki yanka albasa ki zuba sai ki rufe ki bar shi ya tafasa, amma za ki zauna a wurin saboda kar ya zuba, idan ya fara tafasa sai ki fara zuba ruwan alam ko ruwan tsamin duk wanda kike da shi, amma ta ruwan tsami ta fi dadi saboda idan ruwan alam ya yi yawa ya fita yana bata dadinta kadan kadan haka za ki rinka zuba wa za ki ga yana hadewa ruwan yana fita daban haka za ki rinkayi har ta hade.
Sai ki samu matacin kamu ki zuba a ciki ki tace ruwan, sai dan debi tattasai da taruhu da albasa ki jajjaga ki zuba a samanta ki kulle ta za ki iya dorawa a tire sai ki dora mata abu mai nauyi ko kuma ki rataye ta a kusa haka saboda ruwan ya tsane.
Idan ruwan ya gama tsanewa sai ki dakko ki yayyanka ta sannan ki dora mai ki soya.
Bayan kin gama soyawa sai ki gyara sauran kayan wato tattasai da taruhu da dan tumatur da albasa ki jajjaga su, sannan ki soya ki sa magi da gishiri da kori, amma albasar ta yi yawa kada ki sa mata ruwa sai ki zuba wannan awara a ciki ki juya su ya kama jikin awarar.