Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake hada Fuffo:
Abubuwan da za ku tanada:
Fulawa, Sikari, Baikin Fauda ko Yis, Ruwan zafi , Man Gyada, Magi da Gishiri, Madarar Gari da Qwai:
- Terra Ya Yi Nasarar Zama Sinadarin ÆŠanÉ—anon Girki Mafi DaÉ—i A Shekara Ta 2024
- Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Ware Biliyan 19 Don Sanya Wa Lawal Kayan Girki
Ga kuma yadda za ku hada:
Da farko za ku zuba Fulawa a wata roba haka sannan ku kawo Baikin Fauda ko Yis duk dai wanda za ku yi amfani da shi ku zuba, sai ku zuba madara sannan sai Gishiri kadan haka sai Qwai shima ku fasa a ciki, amma kada ya yi ruwa ko kauri kwabin.
Sannan sai ku cuccura shi kamar Bol.
Sai ku dora Mai a wuta ya yi zafi, sannan ku fara soyawa. Bayan kin gama suya shi sai ki barbada masa sikari.
Yadda Ake Hada Fankek da Zuma:
Abubuwan da za ku tanada:
Fulawa, Bakin Fauda, Qwai, Madarar Ruwa, Gishiri, Bota:
Yadda za ku hada:
Za ku samu roba tankade fulawar a ciki duk abin da za ku yi da fulawa a bukata a tankade ta, sannan ku zuba Baikin Fauda da gishiri da madara, sai ku kwaba amma ana bukatar kwabin ya dan yi ruwa-ruwa, ana amfani da madara a matsayin ruwa.
Sannan sai ku dora Mai a wuta ko Bota duk wanda za ku yi amfani da shi, idan ya yi zafi sai ku dinga zuba kwababbiyar Fulawa kuna soyawa, amma ban da juyawa kamar dai yadda ake Sinasir.