Gyaran gashi na da muhimmanci sosai wajen kara wa mace kyau, da cikar darajarta.
Gashi halitta ce, kyauta daga Ubangiji ya ba wasu baki, da mai yawa, da mai tsawo, da kyau. Ya ba wasu ja, da kadan, da karfi, ko da laushi sannan kuma yardar Allah ne, ya ba mu dama ta iya gyara shi.
Ya zama an samu ci gabansa, kuma ya zama cikar kyawunki ko da kuwa ba shi da yawa, Idan kin iya gyara shi wato yana samun kyakkyawar kulawa.
Hanyoyin Gyara Gashi
1- Wanke gashi da ruwan sabulun wanke kai.
2- Amfani da man gashi da ya dace da irin yanayin gashinki.
3- Turara gashi (steaming) da hade-haden gargajiya. Ko kuma da wasu mam zamani .
4- Kitso akai-akai, tare da lura da makitsiyar da hannunta ya karbe ki.
5– Yi wa gashinki addu’a.
6– Cin lafiyayyen abinci da kayan marmari.
7– Idan kina gyaran gashi na konawa (Relader), to dole ne a rika yawan zuwa gidan gyaran gashi akai-akai.