Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake Miyar Margi:
- Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah
- Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025
To, ga yadda ake miyar Margi (wanda ake kira Margi soup a wasu wurare), wato miya ta al’ummar Margi da ake yi a yankin Borno da Adamawa.
Abubuwan da ake bukata:
Nama ko kaza ko kifi, Man gyada ko gyada da aka nika, Daddawa, Yakuwa (ko kubewa, ko danyen ganyen kuka bisa ga nau’in da ake so), Attaruhu da tattasai,
Albasa,Maggi da gishiri, Citta da tafarnuwa (idan ana so)
Yadda ake hadawa:
Da farko za a wanke nama, a saka a tukunya, a zuba albasa, daddawa, maggi da gishiri, a dafa har sai ya fara dahuwa.
Sannan sai a nika kayan miya, tattasai, attaruhu, da albasa tare (idan ana so, a hada da tafarnuwa da citta).
Sai a kaka kayan miya bayan naman ya tafasa, a zuba kayan miya da aka nika a ciki, a barshi ya tafasa sosai. Sannan a zuba man gyada Idan ana da man gyada, a zuba kadan domin miya ta yi taushi da dandano mai dadi.
Idan ba man gyada za, a iya amfani da gyada da aka nika kamar yadda ake miyan gyada. Sai a wanke yakuwa wadda dama anyankata ko kubewa, a zuba cikin miyan, a barshi ya dahu har sai ya yi laushi da kauri.
Sannan a dandana, idan akwai bukatar kari sai a kara maggi da gishiri.
A bar miyar ta tafasa kadan domin ta hade














