Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
- ‘Yan Afirka Da Za Su Haska A Firimiyar Ingila
- Marubuta Na Taimakawa Wajen Bunkasa Rayuwar Al’umma -Miyetti
A yau shafin namu zai zo muku da yadda uwargida za ta hada miyar zogale:
Abubuwan bukata:
Zogale, Nama, Albasa, Attaruhu, Tattasai, Tumatur, Mai, Gishiri, Magi, Kayan Kamshi, Gyada Markadadde:
Yadda za ki hada:
Da farko za ki gyara zogale sai ki ajiye shi a gefe, sannan ki dora tukuya a wuta ki zuba mai idan ya dan yi zafi sai ki yanka albasa ki zuba tare da nama da tattasai da tumatur da attaruhu wanda dama kin riga kin gyara su kin kuma jajjaga su sai ki soya su sama-sama, sannan ki zuba magi da gishiri sai kayan kamshi wanda kike so ki juya su idan suka soyu ya dan yi kauri sai ki sa masa ruwa dai-dai yawan ruwan miyar da kike bukata idan ya tafasa sai ki sa masa gyadar ki barta ta dan dahu idan ta dan dahu sai ki zuba zogalanki juya sannan ki rufe ki barshi ya dahu.
Ana cin miyar zogale da kowanne irin tuwa amma ya fi dadi da tuwan shinkafa.
Idan kina so za ki iya sa wake yana dadi sosai da wake. Idan za ki sa mata wake bayan kin gama soya kayan miyan na ki sai ki zuba ruwa ki sa wake idan waken ya kosa dahuwa sai ki zuba zogalan da gyadar su dahu tare. A ci dadi lafiya.