Masu karanta wannan jarida mai farin jini barkammu da sake haduwa a wani makon inda a yau kuma za mu kawo muku yadda ake yin Samosa.
Ga abubuwan da ake bukata:
1- Flawa kofi 3, Gishiri pinch, 3-Corn flour 4-Ruwa 5-Nama (nikakken nama) ½ kg 6-Attaruhu manya 5 (jajjagaggiya) 7-Albasa matsakaita 2 (a yanka kanana) 8-Carrot Karas babba 1) a yanka kanana 9-Tafarnuwa 10-Curry da thyme 11-Kayan dandano (dunkule 3-4)
Ga kuma Yadda Ake Hadawa
Da farko za ki samu bowl ki zuba fulawa da Corn flour da dan gishiri sai ki kwaba shi kamar yadda ake yin dough da meat pie za ki buga shi sosai har fulawar ta saki jikinta.
Sannan ki yi rolling dinta da fadi kamar Circle ki shafa mai akan daya sai ki barbada fulawa akai, sai ki sake dora wani dough din a haka za ki yi wa dukkansu, sannan sai ki sake rolling dinsu ya yi fadi.
Daga nan ki dora wannan fulawar a kan non stick pan na tsawon mintina 2-5 sai ki sauke ki yanka shi gida hudu, kar a sa wuta sosai (medium heat).
Don yin fillings, ki dafa nama tare da albasa, attarugu, Karas, Tafarnuwa, Maggi, Curry da thyme.
Sai ki dauko ko wane bangare na dough daya ki saka fillings sai ki kwaba flour da ruwa don manne bakin samosa din, sai ki soya samosa dinki a cikin deep frying pan har sai ya soyu.