Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa a wannan mako a cikin shirin mu na Girki Adon Mata. Yau mun kawo muku tsaraba daga kasar indiya, za mu koya yadda ake shayi a indiya wato chai tea.
Abubuwan da za ku tanada:
Danyar Citta, Kanunfari, Masoro, Sukari,Madara, Bushashiyar Ganyan Shayi, Star Anise, Kadamon, Sinamon.
Yadda za ki hada:
Da farko za ki zuba ruwa cikin tukunya sai ki zuba duka kayan da na lissafa amma ban da madara sai ki bari ya tafaso kamar tsawon minti 15 haka. Bayan ya tafaso sai ki ba shi tsawon minti 5 kuma sai ki tace, kayan hadin daga cikin ruwan. Sai ki zuba madarar ki cikin ruwan ki kara kunna wuta ruwan ya tafaso tsawon minti biyu shi kennan kin kamala chai tea dinki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp