Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake saduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu na ado da kwalliya.
Uwargida kin san yadda Coca-cola take wanke bandaki idan ya dafe ko kuma ya yi dauda?
Da farko za ki samu Coca-cola idan za ki wanke bandaki ko kuma wasu suna cewa bayangari to duk dai daya ne idan kika ta shi sai ki zuba Coca-cola a bandaki, za ki bi ko ina ki barbada ta cikin shaddar za ki zuba ta tun daga saman shaddar har ciki haka za ki kwakkwara ta, sannan sai wajen shaddar shima ki kwakkwara ko ina ya samu sai tayils din bango shima za ki zuba amma za ki ga yana zubewa ki bar shi ko yaya ne idan ya taba ya wadatar zai gangaro ya dinga zubowa, amma ko yayane zai tsaya,
Daga nan cikin sink shima ki zuba sai kasan tayils shima haka za ki zuba sai ki sa tsintsiya ki dan barbaza ta ko ina ya ji sai ki bar shi ya yi kamar minti talatin zuwa awa daya kafin nan ya jika sai ki kada ruwan omo ki wanke shi ba sai kin sa haifik ba ko Hypo Coca-cola ma ta wanke bandaki duk ba sai kin sa ba Coca-cola nan ta isa za ki ga yadda bandakinki zai yi fari sosai duk wani dafewa ko dauda za su fita.
Idan kuma kina so ma ya yi saurin fita ba sai kin sha wahala sosai ba za ki iya sa sosan karfe wato sosan wanke tukunyya kina sawa kina far gogawa za ki ga yadda zai fita da sauri. Wannan shi ne sabon salon wanki bandaki.