Bayan da aka shiga babbar kofar wurin tarihi na Yinxu dake birnin Anyang a lardin Henan da ke yankin tsakiyar kasar Sin, za a ga inda aka rubuta kalaman Shugaba Xi Jinping na kasar Sin a kan wani allo, inda a cewarsa, ya dade yana alla-alla wajen ziyartar wurin tarihi na Yinxu. Yau burinsa ya cika. Ya yi fatan kara koyo da fahimtar wayewar kan al’ummar Sinawa sosai. Ana amfani da darasin da aka koya daga tarihi, a kokarin raya wayewar kan al’ummar Sinawa na zamani. Kalamansa suna burge duk wanda ya ziyarci wurin tarihin na Yinxu.
Ranar 28 ga watan Oktoban shekarar 2022 da yamma ne Xi Jinping ya yi rangadin aiki a wurin tarihi na Yinxu, wanda ya ratsa kogin Huanhe a arewa maso yammacin birnin Anyang na lardin Henan.
Wurin tarihi na Yinxu, wanda aka fara ginawa yau shekaru fiye da dubu 3 da suka wuce, a matsayin hedkwata ce a karshen daular Shang, wurin tarihi ne na farko a tarihin kasar Sin, wanda aka ambato shi cikin littattafai, kana an same shi ne daga karkashin kasa. Kalmomi da zanen Sinanci dake kan allunan kashi, da bayan kunkuru da aka samu daga wurin tarihi na Yinxu, sun tabbatar da kasancewar daular Shang, wadda da ma aka ambato ta cikin tatsuniyoyi kawai. Don haka an tsawaita tsawon tarihin kasar Sin har shekaru dubu 1, bisa wadannan kalmomi da zanen Sinanci dake kan allunan kashi da bayan kunkuru.
Yayin da Xi Jinping ya halarci taron bita dangane da gada da raya al’adu a birnin Beijing a ranar 2 ga watan Yunin bana, ya jaddada cewa, al’adun kasar Sin na da dadadden tarihi. Kana kuma wayewar kan al’ummar Sinawa na da zurfi sosai, kuma suna shafar sassa daban daban. Ba za a iya sauyawa, da raya nagartattun al’adun gargarjiyar kasar Sin yadda ya kamata ba, sai an zurfafa fahimtar tarihin wayin kan al’ummar Sinawa daga dukkan fannoni, ta yadda za a kara azama kan raya al’adu na gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, da kirkiro wayin kan al’ummar Sinawa na zamani.

Cikin shekaru 100 da suka wuce, masu nazarin abubuwan tarihi da aka binne karkashin kasa sun sha aiki sosai, sun rika hako da kuma gudanar da nazari kan wurin tarihi na Yinxu, har ma wurin tarihi na Yinxu ya zama wurin tarihi na tsohon birnin Sin a zamanin da, wanda aka fi yawan hakowa da kuma gudanar da nazari a kansa, an fi daukar tsawon lokaci kan wurin tarihi mafi fadi. Nan gaba wannan muhimmin wurin tarihi, wanda ya tabbatar da asalin wayin kan al’ummar Sinawa, da tarihinsa da bunkasuwarsa, zai ci gaba da bayyana sirrin wayewar kan al’ummar Sinawa da kuma yayata asalin ruhin al’ummar Sinawa.
A lokacin zafi, wurin tarihi na Yinxu cike yake da masu yawon bude ido. Rukunonin manyan fadoji, kaburburan sarakuna masu fadi, kayayyakin tagulla masu kyau, kalmomi da zanen Sinanci dake kan allunan kashi da bayan kunkuru masu ci gaba, tsarin sana’o’in hannu inda kowa ke da nasa aiki da sauran dukiyoyin daular Shang masu tarihin shekaru fiye da dubu 3 sun girgiza mutane
A watan Oktoban shekarar 1928 ne Dong Zuobin, mai nazarin abubuwan tarihi da aka binne a karkashin kasa ya fara hako wasu a kauyen Xiaotuncun a arewa maso yammacin Anyang, daga nan ne kuma masu nazarin abubuwan tarihi da aka binne a karkashin kasa na kasar Sin suka kaddamar da aikin nazarin wurin tarihi na Yinxu ta hanyar kimiyya. Kafin wannan kuma, an ambato daular Shang cikin kalmomi fiye da dubu 3 a wani littafin tarihin kasar Sin mai dogon tarihi.

Li Boqian, shehun malami a jami’ar Peking ta kasar Sin, kuma babban mai ilmin kimiyya na aikin tabbatar da kasancewar daulolin Xia, Shang da Zhou ya ce, ya zuwa yanzu babu wurin tarihi da ya fi wurin tarihi na Yinxu muhimmanci a idon masu nazarin abubuwan tarihi da aka binne a karkashin kasa. Wurin tarihi na Yinxu ya tsawaito rubutaccen tarihin kasar Sin zuwa daular Shang. Kana wurin tarihi na Yinxu ya taimaka wajen kirkiro tsarin nazarin daulolin Xia da Shang. Daga nan ne muka fara nazarin wayewar kai a can can can da.
Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ana gado, da raya wayewar kan al’ummar Sinawa daga zuriya zuwa zuriya ba tare da tsayawa ba. Kuma ba za a iya kara fahimtar Sin a zamanin da, da Sin a zamanin yau da kuma Sin a nan gaba ba, sai a kara sanin dogon tarihin kasar Sin ba tare da tsayawa ba.
Mutane suna bin sahun shugaba Xi Jinping, suna kara sanin zaman rayuwar kaka da kakani yau fiye da shekaru dubu 3 a wurin tarihin na Yinxu, inda kuma suka kara fahimtar kalmomin Sinanci mafi dogon tarihi.

Liu Shanshan, mai yin bayani a wurin tarihi na Yinxu, ta sha aiki matuka a kwanan baya. Ta kan yi wa masu yawon bude ido cikakken bayani a kalla sau fiye da 10 a duk rana, tare da yin taki fiye da dubu 20. Ta gaya mana cewa, dalibai da ’yan makaranta sun ziyarci wurin tarihi na Yinxu sun kara sanin al’adun daular Shang sosai, tare da kara fahimtar asalin al’ummar Sinawa da ruhinsu. Ta yadda sun kirkiro tunanin girmama abubuwan tarihi da mutunta tarihi. Sun ji alfahari sosai a matsayin daya daga al’ummar Sinawa.
Kalmomi da zanen Sinanci dake kan allunan kashi da bayan kunkuru, wadanda aka samu daga wurin tarihi na Yinxu, sun fi muhimmanci tsakanin abubuwan tarihi masu dimbin yawa da aka samu a nan. Ko da yake an binne kalmomin a karkashin kasa cikin dubban shekaru, amma a matsayinsu na kalmomin da al’ummar Sinawa suka fara amfani da su a can can can da, da zarar aka hako kalmomin daga karkashin kasa, sai an karanta wasu daga cikin su. Abin mamaki ne ko? Shi ne halin musamman na kalmomin Sinanci.

Masu ilmi daga zuriya zuwa zuriya sun dauki shekaru fiye da 120 suna tattara bayanai, tabbatar da tarihi, binciken ma’anar kalmomin da nazarin tarihin daular Shang, a kokarin tono sirrin wayewar kan al’ummar Sinawa.
A dakin nune-nunen kalmomi na kasar Sin, wadda alama ce ta birnin Anyang, ana nuna tarihin sauyawar kalmomin Sinanci. Ana gwada nagartattun abubuwan tarihi dubbai a wannan dakin nune-nunen kalmomi na kasar Sin. ana kara fahimtar halin musamman na tsarin kalmomin da kuma tarihin sauyawarsu.
Yau a duk fadin kasar Sin mai murabba’in kilomita miliyan 9 da dubu 600, mutane ’yan kabilu daban daban suna tuntubar juna, da mu’amala da juna ba tare da wata matsala ba ta hanyar amfani da kalmomin bai daya, duk da cewa, suna magana cikin yare daban daban, kana suna rayuwa bisa mabambanta al’ada. Me ya sa haka? Saboda kalmomin masu dubban shekaru suna hada su tare.
A lokacin hutu na murnar ranar 1 ga watan Mayun bana, wato ranar kwadago ta kasa da kasa, yawan mutanen da suka ziyarci dakin nune-nunen kalmomi na kasar Sin ya zarce dubu 20 a kowace rana. A wajen dakin kuma, akwai wani lambun shan iska mai ban sha’awa, wadda aka shigar da al’adun kalmomin Sinanci cikin fasalin lambun. Mazauna wurin suna sha’awar yin yawo ko wasa a lambun shan iskar a lokacin dare.
A wurin tarihi na Yinxu, ana kara nuna wa masu yawon shakatawa abubuwan tarihi masu ban sha’awa ta hanyoyi masu kayatarwa. Tsohon wurin tarihin nan ya kyautata surarsa sosai, ta yadda al’umma suna kara sha’awar kawo ziyara. Yanzu ana gudanar da ayyukan gina lambun shan iska na wurin tarihi na Yinxu da kuma garin al’adu, da yawon shakatawa mai taken nazarin abubuwan tarihi da ke karkashin kasa. Har ila yau ana amfani da wasu fasahonin zamani. Alal misali, fasahohin AR, da Holographic display, wajen zamanintar da wurin tarihi na Yinxu don ya biya bukatun masu yawon shakatawa. Ban da haka kuma, wurin tarihi na Yinxu ya sabunta hanyoyin ilmantar da jama’a, yana ta fito da wasu abubuwan al’adu masu matukar ban sha’awa. Alal misali, matasa su kan yi amfani da hotunan kalmomi da zanen Sinanci dake kan allunan kashi da bayan kunkuru masu kayatarwa yayin da suke mu’amala da juna cikin yanar gizo. Wasu kuma suna sha’awar sayen kadarorin yanar gizo dangane da kayayyakin tagulla a zamanin da, wadanda ake adanawa ta fasahar “Block Chain” domin cinikayyar su bisa wasu sharudda.

A cikin dakin nune-nunen kalmomin Sinanci na kasar Sin, ana koyar da kananan yara kalmomi da zanen Sinanci dake kan allunan kashi da bayan kunkuru. Kananan yara suna koyon rubuta kalmomin, yin zane-zanen abubuwa masu halin musamman na daular Shang kan jaka, da koyon yin raye-raye dangane da kalmomin Sinanci. Sun kara fahimtar kyan ganin kalmomin Sinanci da kuma hazakar al’ummar Sinawa cikin wasu wasanni masu kayatarwa. A shekarun baya-bayan nan, dakin nune-nunen kalmomin Sinanci na kasar Sin ya kaddamar da ayyuka fiye da 160 dangane da ilmantar da jama’a kan kalmomin Sinanci, da harkoki masu ruwa da tsaki fiye da 1500, inda iyalai kusan 45000 suka shiga.
A wurin tarihi na Yinxu da ke birnin Anyang, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, dole ne mutanen Sin su karfafa imaninsu kan al’adunsu, su karfafa gwiwarsu, da kuma yin alfahari a matsayinsu na Sinawa.
(Mai fassarawa: Tasallah Yuan daga CMG Hausa)