An tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da wasu biyu suka ɓace bayan ambaliyar ruwa ta tafi da su biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a garin Zaria na jihar Kaduna a ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Lamarin ya faru ne a unguwar Tudun Jukun da ke Zariya, inji rahoton Daily Trust.
- IATF 2025: Zamfara A Shirye Ta Ke Wajen Maraba Da Masu Zuba Jari – Gwamna Lawal
- Kwankwaso Ya Gana Da Shugabannin NNPP A Kuros Ribas Don Tunkarar Zaɓen 2027
An kuma gano gawar wata budurwa ‘yar shekara 18 mai suna Fatima Sani Dan Marke dalibar makarantar koyon ilmin ta Funtua da wani dalibi Yusuf Surajo wanda aka fi sani da Abba a gadar makarantar firamare ta Isan Nabawa da ke Tudun Wada, Zariya.
Yayin da aka gano gawar Surajo a ranar Litinin, an gano gawar Fatima washegari, Talata. Sai dai har yanzu ba a gano gawar kanwar Fatima ‘yar shekara uku, Haneefa ba.
A lokacin da lamarin ya faru, Fatima tana goye da kanwarta Haneefa mai shekaru uku a duniya.
Su biyun suna dawowa ne daga gidan kakarsu da ke Magume zuwa gidan su da ke Tudun Jukun.
Malamin Islamiyyar su Fatima, mai suna Malam Daddy ne ya yi musu rakiyar hanya acikin kekensa mai taya Uku (Keke-napep).
Shaidun gani da ido sun ce, abin takaicin ya afku ne a mahadar da ke kusa da Cocin Nasara Baptist da ke kan hanyar Gaskiya babban layi a Tudun Jukun.
Sun ce yayin da direban keken, Malam Daddy ya tsallake rijiya da baya, amma Fatima da karamar kanwarta, Haneefa ruwan ya tafi da su.
Shaidan ya ci gaba da cewa, wani mutum da ya garzaya wurin don ya cet su, shi ma ruwan ya tafi da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp