Amurka ta fara aiki da dokar da ta zartar, na wai “Dokar Hana Aikin Tilas Ga Al’ummar Uygur” a kwanan baya.
Bisa ga dokar, hukumar kwastam da tsaron kan iyakoki ta kasar Amurka, ta ayyana dukkan kayayyakin da ake samarwa a yankin Xinjiang na kasar Sin a matsayin wai kayayyaki na “aikin tilas”, tare da hana shigo da duk wasu kayayyaki dake da nasaba da Xinjiang cikin Amurkar.
Duk da cewa, tuni an fara yawan yin amfani da injuna wajen noman auduga da ma sauran fannoni, a yayin da ake kare hakkin ‘yan kwadago ‘yan kabilu daban daban na Xinjiang yadda ya kamata, amma ‘yan siyasar Amurka ba su kula ba, har suka yayata karairayi na wai “aikin tilas” a yankin Xinjiang a yunkurin shafa wa kasar Sin bakin fenti.
Sai dai ba wai damuwa da yanayin da ‘yan kwadagon yankin ke ciki ‘yan siyasar Amurka suke yi ba, hasali ma dai, suna fakewa da sunan kare ‘yancin dan Adam don neman tada rikici a Xinjiang, ta yadda za su cimma burin dakile ci gaban kasar Sin bisa wai “batun Xinjiang”.
Wannan mataki ba wani sabon abu ba ne, idan ba a manta ba, don neman kaddamar da yaki a kasar Iraki, Amurkar ta taba yin amfani da farin garin da ba a tabbatar da yanayinsa ba wajen zargin Irakin da mallakar makaman kare dangi, tare da jefa kasar cikin tashe-tashen hankula, baya ga fararen hula sama da dubu 200 da suka mutu a kasar.
A kuma duba yanayin da kasashen Afghanistan da Syria da Libya ke ciki, lallai Amurka ta lalata zaman lafiya a kasashen ta hanyar nuna fin karfi da ma daukar wasu matakai na rashin kunya.
‘Yan siyasar Amurka sun sha yin haka, amma a wannan karo, kasar Sin ba za ta bar su su ci nasara ba.
Aminai masu bibbiyarmu, mun san kun sha karanta rahotanni da ke shafa wa hakkin dan Adam na Xinjiang bakin fenti, amma sai a yi hankali, a bambanta karya da gaskiya, don kada a bar mai karfi ya yi duk abin da ya ga dama.
Gani ya kori ji, Xinjiang na muku maraba da zuwa, don ku gani da ido yadda ake samun zaman lafiya da ci gaba da ma yadda al’umma ‘yan kabilu daban daban ke zaune lafiya da juna a yankin. (Mai Zane: Mustapha Bulama)