Za a iya cewa wasan yau da aka buga tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu na Arsenal da Real Madrid ya zamo wasa mafi kayatarwa da aka buga a wannan kakar a gasar Zakarun Turai (UEFA).
Wasan da aka buga a filin wasa na Emirates dake birnin Landan ya matukar kayatar da masu sha’awar kwallon kafa a fadin Duniya, ta wani bangaren kuma wasan bai yi wa wasu dadi ba musamman magoya bayan Real Madrid.
- Ko Raunin ‘Yan Wasa Zai Rage Wa Barcelona Karsashi A Kakar Bana?
- Za Mu Doke Atletico Madrid Har Gida, Hansi Flick
Shekaru 6 kenan rabon da kungiyoyin biyu su hadu da juna, kuma shekaru 19 rabon da su hadu a gasar Zakarun Turai, amma kuma Arsenal ta kuma tabbatar da cewar har gobe ruwa na maganin dauɗa bayan da ta lallasa zakarun gasar da ci 3-0 a Emirates.
Declan Rice ne ya jefa ƙwallaye biyu a wasan kafin Mikel Merino ya jefa ta uku kuma ta ƙarshe a wasan, hakan ya sa Rice ya zamo dan wasa na farko a tarihin gasar Zakarun Turai da ya ci ƙwallaye biyu daga bugun tazara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp