Tsawon shekaru 7 kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shafe tana jiran samun damar dawowa gasar zakarun Turai tun bayan da Bayern Munich ta zazzaga mata kwallaye 10 a wasanni biyu da suka buga a shekarar 2017.
Sai a wannan shekara ta 2024 kungiyar ta Ingila ta samu damar buga gasar zakarun Turai bayan ta kare a matsayi na biyu a teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila,amma kuma har wayau Bayern Munich ta kuma fitar da Arsenal daga gasar ta bana.
- Mutane 7 Ne Suka Rasu Sakamakon Zazzabin Cizon Sauro Da Taifod Ba Wata Sabuwar Cuta Ba – Gwamnatin Kano
- Idan Isra’ila Ta Kai Wa Iran Hari Ba Za Mu Goya Mata Baya Ba – Amurka
A farkon wannan kaka ta bana magoya bayan Arsenal sunyi murnar ganin kungiyar da suke goyon baya ta tsallaka zuwa matakin zagaye na 16 na gasar bayan ta jagoranci rukunin B,Arsenal ta kuma doke FC Porto a wasan zagaye na 16.
Magoya bayan sun fara fitar da rai daga zuwan kofin gasar zakarun Turai karo na farko a tarihi zuwa filin wasa na Emirates Stadium bayan da aka hada Arsenal da Bayern Munich domin buga wasan zagayen kwata fainal,inda suke ganin zakarun na Jamus a matsayin wata annoba a wajensu ta fuskar kwallon kafa.
Hakan dai ta faru inda Bayern ta doke abokiyar karawarta Arsenal a filin wasa na Allianz Arena dake Munich da ci 1 mai ban haushi bayan an buga kunnen doki a gidan Arsenal a farkon wannan wata da ci 2-2.