Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) sun kama wasu mutane uku da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da alburusai a jihar Kaduna.
A cewar hukumar, an kama mutanen ne a yayin gudanar da binciken ayyukan ta’addanci a kananan hukumomin Igabi da Kachia na jihar.
- Gwamna Abba Ya Jaddada Mubaya’arsa Ga Kwankwaso
- NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa
A cikin wata sanarwa da ‘yan jarida suka samu, DSS ta ce daya daga cikin wadanda ake zargin, dan shekara 30, an kama shi ne a hanyar Nnamdi Azikiwe Bypass da ke Igabi a lokacin da yake dauke da bindigogi kirar AK-47 guda biyu, bindigar PKT daya, harsasai na kisa sama da 200, da kuma mujallu hudu a boye a cikin buhunan masara.
Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf.
Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar.














