Ga duk mai biyiyar manufofin kasar Sin na samar da ci gaba, ba zai gaza sanin shirin kasar na daidaita harkokin zuba jarin waje na shekarar nan ta 2025 da aka fitar ba, wanda ke kunshe da manufofi 20 da aka kasa cikin muhimman fannoni 4, wadanda suka hada da fadada bude kofa bisa radin kai, da kyautata damammakin zuba jari, da daga matsayin dandalolin bude sassan tattalin arziki, da kara inganta tsarin samar da hidimomi masu nasaba.
Masharhanta da dama na kallo wannan shiri a matsayin manuniya, dake kara tabbatar da burin kasar Sin na dada bude kofofinta ga sassan kasa da kasa.
- Sojoji Sun Kashe Ƙwararren Mai Haɗa Wa Boko Haram Bam A Borno
- Sin Za Ta Kara Ingiza Samar Da Kudaden Gudanar Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu
Kamar dai yadda muka sani, batun bude kofa na kan gaba cikin manufofin kasar Sin na samar da ci gaban kasa, kana hakan daya ne daga ginshikan zamanantarwa irin ta Sin. Kazalika, turba ce ta samar da wadata, da bude sabbin babuka na cimma nasarar zamanantarwa irin ta Sin.
Karkashin hakan, kasar Sin ta shafe sama da shekaru 40 tana ta aiwatar da managartan matakai, kama daga bude yankunan musamman na raya tattalin arziki, zuwa bude yankunan gwaji na gudanar da cinikayya maras shinge, da aiwatar da shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya” ko BRI. Dukkanin wadannan matakai ana daidaita su ne da dunkulallen tsarin raya tattalin arzikin duniya, tare da fitar da sabon salon hadin gwiwar kasa da kasa.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta himmatu wajen aiwatar da manufofin kara bude kofofinta, ta kuma cimma manyan nasarori sakamakon aiwatar da sauye-sauye. Har ila yau, tana ta aiwatar da matakan zurfafa bude kofa a karin sassan samar da ci gaba.
Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke kara samun tagomashi, masana daga sassa daban daban, na ganin hakan dama ce ta ci gaban duniya baki daya. Kamar dai yadda sakamakon wani bincike, na asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna yadda bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ke shafar ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Binciken ya nuna bunkasar tattalin arzikin Sin da karin kaso daya bisa dari, yake haifar da matsakaicin bunkasar tattalin arzikin sauran sassan kasa da kasa da kaso 0.3 bisa dari.
Duba da haka, ma iya cewa duniya za ta ci gaba da shan romon bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, yayin da kasar ke ta kara fadada manufofinta na bude kofa ga sassan duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp