Yawan kudin tikitin kallon fim din “Ne Zha 2” na kasar Sin da aka saya ya zarce dala biliyan 16 a daren jiya, abin da ya sa ya shiga sahun fina-finai 9 mafi samun yawan kudin tikitin kallon fim dake sahun gaba a duniya. Dalilin da ya sa fim din samun wannan ci gaba shi ne ingancin abin da ya kunsa.
Labarin da wannan fim ya gabatar ya yi daidai da wasan yanar gizo mai suna “Black Myth: Wukong”, wanda shi ma na kasar Sin ne. “Ne Zha” da “Wukong” dukkansu jarumai ne dake cikin tatsuniyar gargajiya a dogon tarihin Sin, wadanda ba su mika wuyansu ga makomar da aka tanade su ba, kuma suka yi kokarin rike da kaddararsu a hannunsu duk da dimbin kalubale da wahalhalu a gabansu, inda aka gabatar da labarunsu bisa tunani irin na zamanin nan, wadda hakan ya sa al’ummar duniya suka yi saurin fahimtar abin.
Idan aka duba bangaren fasahar zamani ta wannan fim, za a ga cewa, an kwashe shekaru 5 ana tsara fim din na “Ne Zha 2”, wanda ya kunshi hotuna na musamman kusan 2,000 da wasu abubuwa na musamman masu tasiri a shirin fim sama da 10,000. Matakin da ya nuna cewa, fina-finan Cartoon da Sin ta kirkiro ba kawai sun amfani da fasahar waje ba, har ma a yanzu sun iya zama ma’aunin da za a yi misali da shi.
Ban da wannan kuma, fim din ya bayyana dankon zumuncin iyali da abokai masu nuna zaman tare da zuciya daya, kuma ya nuna yadda mutanen fim din suka yi iyakacin kokarinsu wajen kare garinsu da iyalansu, abin da ya dace da nagartaccen tunanin Bil-Adama na bai daya. Shi ya sa fim din ya zama mai taba zuciyar masu kallo na kasa da kasa. Abin da kuma har ila yau ya nuna cewa, zuciyoyin Bil-Adama a kusa suke da juna, wadda hakan ke iya daidaita mabambantan ra’ayoyin al’adu a tsakanin kasashe daban-daban, da kara mu’amala da cudanyar al’ummun duniya. (Amina Xu)