Manajan gudanar da ayyuka, kuma babban jami’i a fannin hada jinsin dabbobi, Mista Jonathan Jatau ya sanar da cewa; idan aka bai wa Fulani Makiyaya kwarin guiwa ta hanyar yin amfani da dabarun zamani na amfani da jinsin shanu, wato ta hanyar sanya maniyin wata saniya zuwa cikin mahaifar wata saniyar, hakan zai taimaka wajen kara samar da madarar shanu.
Kazalika, ya sanar da cewa; hakan zai kuma taimaka wajen kara samar da naman shanu mai yawa da kuma rage rikice-rikice a tsakanin manoma da Fulani Makiyaya a fadin wannan kasa.
- Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe
- Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole
Jatau ya bayyana hakan ne, a taron bita da aka shirya wa wasu Fulani Makiyayya, kan muhimmancin yin amfani da maniyin saniya da aka shirya wa masu kula da ayyukan kiwo a karkashin shirin kiwo na ‘L-PRESS’ da aka gudanar a garin Minna na Jihar Neja.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da kokari don ganin an iske masu yin kiwon shanu a kasar nan, domin fadakar da su kan muhimmancin rungumar wannan tsari na zamani.
Sai dai, ya yi nuni da cewa; wasu al’adu na haifar da tarnaki a tsakanin wasu masu kiwon a kasar na rungumar wannan tsarin.
“Na ga wasu gidajen gona da ake yin irin wannan dabara ta zamani, sannan kuma ana bayar da kulawar da ta kamata; wanda hakan ya sanya ake iya samar da litar madarar shanu daga tsakanin lita 15 zuwa 30,” in ji Jatau.
“Akwai wasu Fulani Makiyaya ‘yan kalilan da suka rungumi wannan tsari, misali a Jihar Bauchi; inda wani makiyayi ya rungumi wannan tsari tare kuma da amfanarsa yadda ya kamata,” a cewarsa.
“A lokacin da muka gudanar da ayyukanmu, wasu daga cikin Fulani Makiyaya, sun zo sun saurari wannan batu na dabara ta zamani tare da shanunsu, mun kuma aiwatar da tsarin a kan shanun nasu, inda daga baya suka ga yadda madarar shanunsu ta kara habaka,” in ji shi.
Jatau ya kara da cewa, suna kan ci gaba da bai wa Fulani Makiyaya kwarin guiwa, kan rungumar wannnan tsari, sai dai, wasu na fuskantar kalubale na kula da shanunsu da aka dora su a kan tsarin.
“A wasu kasashen na Afirka za ka cewa, Makiyayin da suka rungumi wannan tsari, na da shanu uku ne kacal da daukacin iyakansa suka dogara a kansu, wanda hakan ke ba su dama a kullam na samar da litar madara daga tsanakin 15 zuwa 20, “ a cewarsa.
Ya kara da cewa, hakan ya sanya a kullum suke samar wa da kansu dimbin riba, wanda kuma hakan ya sa ba su dogaro da aikin gwamnati ba kwata-kwata.
Ya yi nuni da cewa, idan har a raba daya za ka sayar da litar madara daya kan Naira 1,000, a wata za ka iya samun kudin shiga da suka kai Naira miliyan 1.8 da shanu uku kacal.
Ya ci gaba da cewa, da wannan ribar kadai za ka iya ci gaba da ciyar da shanun da lula da lafiyarsu da biyan ma’aikatan da ke kula da su da kuma daukar sauran dawainiyar kula da iyalanka.
Ya bayyana cewa, duba da cewa; ana fuskantar matsalar wajen da dabbobi za su yi kiwo a kasar nan, amma idan Fulani Makiyaya suka rungumi wannan tsari, hakan zai rage yawan samu rikice-rikice a tsakanin manoma da Fulani Makiyya a kasar.
Kazalika, ya sanar da cewa; idan masu kiwon suka dauki wannan tsari za a samu cewa, alfanun da za su samu ya dara irin na kiwon gargajiya da ake yi a cikin kasar.
Jatau ya bayyana cewa, wannan tsarin abu ne da ke da tsawon tarihi a kasar nan, domin an faro shi ne tun a shekarar 1949; tun bayan da aka dauki nau’in na jinsin daga wata gona da ke garin Shika a birnin Zaria, aka kuma kai shi zuwa cibiyar gudanar da bincike kan lafiyar dabbobi ta Bom.
Sai dai, ya bayyana cewa; rashin ci gaba da bibiyar wannan tsare-tsaren daga bangaren gwamnati, hakan ya haifar da koma baya ga wannan tsair.