Tattaunawa game da yunwar da ake fama da ita a Nijeriya, musamman yadda matan aure da ‘yan mata suke ta zinace-zinace don kawai su ciyar da kansu, da kuma yadda maza suke guduwa suna barin iyalansu cikin yunwa, wasu kuma suna zaune a gida ba tare da sun samu damar fitar ba wani ko ya fita mma ba lallai ne ya samo ba.
Me za a ce a kan hakan?
Wane irin kira za a kara yi ga gwamnati don shawo kan matsalar, kuma ta wacce hanya ake ganin za a iya shawo kan wannan matsalar. Kazalika wadanne irin shawarwari za a ba wa mata da maza magidanta har ma da ‘yan mata, musamman masu je fa rayuwarsu cikin wani hali saboda neman abin da za su ci?
Bilkisu Maharazu
A gaskiya wannan matsalar da Nijeriya take ciki duk magana daya ce dai a kan farashin mai fetur domin da ba’a cire wannan tallafin man fetur din ba da haka ba ta faru ba, domin karin man da Nijeriya ta yi ya yi yawa kusan duk bayan dan lokaci sai an kara.
Bugu da kari, duk lokacin da man fetur ya hau sai kaya sun tashi duk da dai suma ‘yan kasuwa suna da nasu laifin domin wani lokaci abin da bai kai a ce ya kai haka ba sai ka ji ya kai, amma Gwamnatin Nijeriya ita ce babbar mai laifin domin da ba’a kara ba da haka ba ta faru ba.
Don haka hanyar da za a bi a magance wannan matsalar kawai ita ce, sai dawo da farashin mai, ko kuma in ce maida tallafin da shugaban kasa ya janye har tsawon shekara da watanni da ya yi, domin wannan shi ne ummul haba’isin da haddasa hakan, Sannan fitintinu da yunwa da ake fama da su a Nijeriya, cire tallafin man fetur ko kuma karin fara shin mai da aka yi duk shi ya haddasa wadannan matsaloli da ake ciki wadanda suka hada da yunwa, sace-sace da sauransu, shawarata da zan ba wa maza da mata magidanta da ‘yanmata musamman masu jefa rayuwarsu cikin wani hali saboda neman abin da za su ci da su ji tsoron Allah a duk inda suke kuma a yi hakuri da abin da ya samu idan da ka saba da facaka da kudi yanzu sai ka rage, haka kuma abin da ya samu da shi ake amfani don haka ina kira da ‘yan uwa maza da mata da mu yi hakuri da halin da muka samu kanmu a ciki kuma mu rika addu’a Allah ya kawo mana karshen wadannan matsalolin.
Usman Sani
Wannan yanayi abin takaici ne matuka kuma yana nuna irin tsananin matsalar tattalin arziki da yawa daga cikin iyalai a Nijeriya ke fuskanta. Gaskiyar cewa mata da ‘yan mata suna fadawa cikin yanayin karuwanci don kawai su rayu, kuma maza suna barin iyalansu, yana nuna irin tsananin yunwa da rashin aikin yi da ake fama da su. Wannan alama ce ta rugujewar zamantakewa da tattalin arziki, kuma ya kamata a dauki matakin gaggawa don magance ta.
Za a iya yin kira ga gwamnati ta samar da karin damar ayyukan yi, musamman a fannonin da za su dauki ma’aikata da yawa kamar noma, masana’antu, da gina-gine. Haka nan, ya zama dole a dauki matakan taimako kai tsaye don samar da abinci da kayan bukatu ga al’ummomin da suka fi kawo rauni. Kafa tsare-tsaren kariya ta zamantakewa da tallafa wa iyalai masu fama da matsaloli zai taimaka wajen rage yunwa da matsi.
Kazalika za a iya magance wannan matsala ta hanyar amfani da dabaru na gaggawa da na dogon lokaci. A takaice, a samar da tallafin abinci na gaggawa da shirin tallafi na kudi ga iyalan da suke cikin matsananciyar bukata. A dogon lokaci, samar da ayyukan yi, koyar da sana’o’i, da kuma shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki za su taimaka.
Hasan Tijjani
To mutane suna fama da kansu suna cikin mawuyacin hali mutane suna cikin takaici sannan su kadai suka san halin da suke ciki na yuwa da fatara da tsadar rayuwa. Muna kira da babbar murya ga gwamnati da ta dubi wannan yanayi da ake ciki na rayuwa, wasu sau daya suke samun abin da za su ci kuma ba wai a koshi ba, wani haka zai wayi gari bashi da abin da zai ci sai an nema. Dan Allah gwamnati ta duba wannan yanayi na rayuwa a tausaya wa al’umma.
Hanyar da za a iya shawo kan wannan matsalar itace gwamnati ta yi kokarin ta duba wannan al’amarin, sannan a dawo da tallafi idan za a dawo da tallafin mai to ina ganin wannan matsalar za a kawo karshenta in sha Allahu za a samu saukin rayuwa abinci zai sauko sauran kayayyaki za su sauko za a samu sauki zirga-zirga.
Shawarar da za a ba wa ‘yanmata ita ce, su dubi halin da ake ciki su rage dogon buri sannan kuma duk abin da ya zo su dauke shi a matsayin kaddara musamman yanayin da ake ciki na rashin wadata da sauransu, sai a rage dogon buri duk abin da ya zo a yi hakuri. Su kuma magidanta yanzu misalin lokaci ne ba na haihuwa ba, ya kamata a dan tsagaita har a ga abin da hali zai yi, sannan su ji tsoron Allah su daina gudu suna barin mata da dawainiya a tausayawa matan kai da kake namiji ka gudu to ballantana mace wacce kila ita ba ta da aikin yi kila sai ‘yar wata sana’a karama haka? To don Allah a ji tsoron Allah a bar guduwa a zauna a koka tare.
Jibril Muhammed
Ya kamata duk runtsin rayuwa abu mafi dacewa shi ne duk halin da mutum ya samu kansa a matsayin sa na namiji wani ya kan zama maigida ne ko saurayi, abu mafi dacewa ya tsarawa kansa rayuwa tun farko, wajen samun sana’ar yi ya koye ta, idan kuma aiki ne to nan ma haka lamarin, sai ya bi a hankali, kada ya sa karya ya yi komai daidai ruwa dai dai tsaki. Mace wata ta kan kasance tana da aure ko budurwa babban lamari shi ne hakuri a rika jiran lokaci, ba ma kamar irin wannan lokaci da rayuwa ta yi tsada abubuwa sai a hankali.Idan kuma budurwa ce sai ta yi hakuri da abubuwan da take samu a gida, ta kuma samu sana’ar yi ta hannu.
Abdurrahman Tijjani
Gaskiya wannan hali da aka jefa Nijeriya ko in ce mutanen Nijeriya abin takaici ne sannan kuma abin a jajanta mana ne a tausaya wa marasa karfi, sannan kuma a karfafa wa masu kudi gwiwa na su rika taimakawa talawa a hada da addu’a kafin Allah ya kawo mafita.
Mutane suna cikin wani hali suna cikin mawuyacin yanayi ina ganin kila tun da ake ba a taba fadawa irin wannan yanayi da ake ciki ba na yunwa da tsadar rayuwa, sai dai mu ce Allah ya kawo mana sauki da mafita.
Muna kiran gwamnati da ta taimaka ta san halin da al’umnar ta ta shiga a san abin da yakama a yi a tausayawa talakawa a sassauta wannan yanayi da ake ciki, imma dai na tallafawa ne ko kuma idan zai yiwu wannan tallafi da aka cire a dawo da shi ko za a samu sauki.
Shawarar da za a ba wa ‘yan mata da zawarawa su yi hakuri komai ya yi zafi maganinsa Allah a yi ta addu’a in sha Allahu Allah maji rokon bawansa ne a koma ga Allah mu yi ta istigfari Allah zai kawo mana sauki da yardarsa.