- Al’amarin Ya Fi Kamari A Kan Kananan Kudade
- Duk Da Sabon Umarnin CBN, Abin Na Ta’azzara
Har yanzu dai tsugune ba ta kare ba a kan karancin takardun kudin da al’umma ke fuskanta a kasar nan, bisa yadda mutane ke gamuwa da cikas a kokarin karbar kudi a bankunan kasuwanci duk kuwa da hukuncin kotun koli na cewa a ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi har illa ma sha Allahu.
Abokan hukdar bankuna da masu harkar POS na ci gaba da korafi a kan sabon umarnin da Babban Bankin Nijeriya CBN ya ba bankunan kasuwanci na rage kudaden da suke karba a rana da kashi 50. A wasu jihohin ma bankuna sun kayyade tsabar kudin da za a iya karba a rana zuwa Naira 5,000.
Sai dai kuma babban bankin ya ba bankuna umarnin dakatar da karbar kudin haraji a kan masu kai ajiiyar manyan kudade a banki. A halin yanzu kofa a bude take ga duk wanda yake son ajiye kudi a banki komi yawansu, ba tare da ya biya haraji ba. Babban banki ya fito da wannan matakin ne don kawo karshen matsalar karancin takardar naira a sassan Nijeriya.
CBN ya nemi ‘yan Nijeriya da ka da su firgita don ya yi tanadin issasun kudade da za su iya cimma bukatun al’umma a saboda haka ya umarci bankuna kasuwanci su sake jiki su ci gaba da biya wa abokan huldarsu bukata ba tare da jinkirtawa ba.
Don jin yadda lamarin yake a wasu sassan Nijeriya, wakilanmu sun tattauna da masu ruwa da tsaki a jihohinsu don fahimtar yadda karancin takardar naira da kuma wannan sabon umarni na CBN na kayyade kudin da abonkan huldar bankuna za su iya karba a rana ya shafi rayuwarsu. Musamman ganin yadda wannan tsarin ya shafi masu manya da kananan kasuwanci.
Kano
Karancin Kudi A Hannun Jama’a Na Kara Ta’azzara
Duk da umarnin CBN na cewa kowa ya ci gaba da karbar kudaden da ake tunanin daina amfani da su zuwa karshen watan Disambar 2023. Har yanzu jama’a a Jihar Kano na fuskantar matsanancin karancin Kudi lakadan wanda hakan ke neman mayar da hannun agogo baya.
A kasuwannin Kano abubuwa sun fara sauyawa, domin wadatar takardun kudin ya fara tarnaki ga harkokin cinikayyar yau da kullum, musamman kasuwannin kauye, masu fito da kaya domin sayarwa inda ake matsa masu lambar karbar ‘transfer’, sannan akwai babbar matsalar karancin kananan kudi irin Naira 20 50 da 100. Kuma wadannan su ne ake amfani da su wajen kananan ciniki a cikin unguwanni da wuraren ‘yan tebura.
Alhaji Mustapha Abdurrazak, dan kasuwa da ke fataucin kayan abinci daga Kasuwannin Kwanar Dangora, Tudun Wada, Sabuwar Kaura da sauransu, ya bayyana cewa rashin kananan kudade na neman hana masu kananan sana’u gudanar da sana’unsu wadanda daman ana sayen kayan nasu ne daga Naira hamsin zuwa dari, musamman kayan cimaka irin awara da dan bagalaje.
Shi ma Alhaji Sunusi Umar Ata dan kasuwa a Kasuwar Kwari cewa ya yi cikin abokan cinikayyarsu idan aka kasa su gida goma, takwas daga ciki ‘transfe’r suke masu maimakon biyan tsabar kudi, “Idan muka tambaye su, cewa suke suna jin tsoron kila fa maganar daina amfani da tsoffin kudade na nan, duk da bayanan da babban bankin kasa ke ta nanatawa cewa za a ci gaba da amfani da tsoffin kudaden.”
Yanzu haka dai da yawa daga cikin Jama’a sun shiga tsaka mai wuya, bangaren masu musayar kudade (canji) su kuma kasuwa ta fara budewa, domin har an fara karin farashi ga mai son a bashi canji kudi a hannu.
Kaduna
Bankuna Ba Su Zuba Wadatattun Takardun Kudi A ATM Ba
Bisa binciken da LEADERSHIP Hausa ta gudanar a Kaduna, masu hulda da bankuna a jihar na fuskantar karancin samun takardun kudi, musamman a tsakanin masu hada-hadar kasuwanci.
Wani dan kasuwa Kabir Sani ya bayyana wa wakilinmu cewa, yana fusakantar kalubalen rashin samun gundarin takardun kudade idan ya je cire kudi a na’urar ATM musamman saboda adadin da bankin CBN ya gindiya wa jama’a na cire kudi.
Wata mai sayayya da wakilinmu ya ci karo da ita, Naomi Daniel ta bayyana cewa, ta je cire Naira 40,000 a ATM don zuwa cin kasuwa, amma sai ta iske bankin ya tsara na’urarsa ta ATM dinsa kan Naira 10,000 kacal za a iya cirewa.
Binciken da LEADERSHIP ta gudanar a wasu bankuna, ya nuna cewa, wasu bankunan na kasuwanci ba su zuba wadatattun takardun kudi a na’urarsu ta ATM ba. Bugu da kari, a jihar, Naira 500,000 kacal wasu bankunan ke yarda a cire in an shiga cikin bankin.
Ita ma wata da aka zanta da ita, Maman Iyabo ta danganta karancin samun kudin da shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara da ke kara karatowa, ganin cewa, a wannan yanayin, musamman mabiya addinin Kirista, na bukatar takardun kudi ne, a hannu don yin amfani da su kai tsaye, maimakon su tura kudaden in sun yi wata siyayya.
Musa Lawal wanda ke zuwa kasuwanni don cin kasuwar kauyuka ya ce, a yanzu ana cikin rani ne kuma wasu manoman da suka girbe amfanin gonakansu, musamman a kauyuka, sun fi son a ba su gundarin kudi a hannunsu, kafin su sayar da amfaninsu, domin ba su yarda da a tura masu kudin ta asusun ajiyarsu na bankuna, saboda matsalar sadarwa, wadda ba lallai ne, nan take kudin su shiga cikin asusun na ajiya a bankunansu ba.
Malam Bala Awwal wanda dan kwangila ne ya ce, dole sai da gundarin takardun kudi yake biyan leburorinsa, domin akasarinsu, ba su da asusun ajiya a bankuna, shi ya sa karancin takardun kudin ke kara haifar da matsi ga ayyukansu.
Adamawa/Taraba
Takardun Kudaden Naira Sun Karanta A Hunnun Jama’a
Jama’a mazauna jihohin Adamawa da Taraba da ke Arewa Maso Gabashin Nijeriya, sun koka da karancin takardun Naira, lamarin da ya haifar da koma baya ga walwalar mazauna jihohin biyu.
Ahmad Nasidi, mazaunin Yola fadar jihar Adamawa, ya ce “Maganar takardun kudi a Adamawa kan sai hakuri, domin babu su, abin da yake akwai sai dai a yi hakuri a ci gaba da lallaba rayuwa a haka, amma babu kudi kam wallahi” in ji Nasidi.
Da shi ma yake magana kan batun, AbdulKarim Jalingo, ya ce “gaskiya ba kamar kwanakin baya ba, kwanaki karancin takardun kudin da dan sauki, amma yanzu suna wahala, domin yanzu za ka ga masu sana’ar POS, suna bin mutane wajen sana’o’i da shaguna suna neman ‘cash’.
“Wasu ma idan an samu tsabar kudin har suna ba da wani abu a ba su kudin, ka ga wannan ya nuna kudi ‘cash’ din yana wahala, ba kaman da ba, sannan takardun naira 100, 50 sun fi wahala a hannun mutane” in ji AbdulKarim.
Zamfara
Rashin Kudi A Hannun Jama’a Na Kawo Wa Kasuwanci Tarnaki
Duk da bayanin da gwamnatin tarayya ta yi na ci gaba da amsar tsafin, yanzu haka a Jihar Zamfara, kudi a hannu sun zamo matsala, hatta a bankuna ma in dai kana son kudi sama da 200,000 sai mutun ya jira a kanta jama’a su kawo a harhada masa musamman ‘yan kasuwa masu zuwa kasuwannin kauyuka, don haka rashin kudi a hannun na neman kawo wa kasuwancin nasu tarnaki.
Yanzu haka masu shagunan POS da yawan su suna hada kai ne da manyan ‘yan kasuwa na cikin gari da ke ba su tsabar kudin don samun riba.
Su kuma manyan ‘yan kasuwa masu sana’ar hatsi, suna zuwa gidajen man fetur don samun kudin a hannu da zuwa cin kasuwanni. Rashin kudi a hannun da kananan canji kamar naira hamsin da ashirin da goma da naira biyar na sanya farashin kayan na canzawa.
A binciken da wakilinmu ya yi, hatta bankuna a jihar na fama da rashin takardun kudi wanda ke jawo matsala ga kananan ‘yan kasuwa a Jihar ta Zamfara.
Borno Da Yobe
Jama’a na kokawa kan karancin takardun kudin
Mazauna jihohin Borno da Yobe da ke Arewa Maso Gabashin kasar nan na ci gaba da kokawa dangane da matsalolin karancin takardun kudade a hannun jama’a, al’amarin da aka bayyana da cikas a harkokin cinikayyar yau da kullum.
Matsalar tana shafar tattalin arzikin jama’ar yankin, wanda sau-tari hakan ke kawo tsaiko tare da tarnaki a jindadin zamantakewa da walwalar jama’a- musamman kananan takardun kudaden naira 50, 100, 200 wadanda su ne aka fi amfani da su a huldar cinikayyar yau da kullum da jama’a ke gudanarwa.
LEADERSHIP Hausa ta leka kasuwar bayan Tasha da ke cikin birnin Damaturu a jihar Yobe, inda jama’a ke gudanar da hada-hadar cinikayyar kayan abinci da masarufi. Ta gano baki daya; ‘yan kasuwa da masu sayen kaya na korafin karancin takardun kudaden a hannun jama’a tare da kira ga gwamnati, bankuna su duba wannan al’amarin.
Hajiya Fadila Usman, wadda aka tarar ta yi cirko-cirko wajen masu sayar da kayan miya saboda rashin tsabar kudin a hannu, ta bayyana cewa “Gaskiya a ‘yan kwanakin nan muna fuskantar karancin takardun kudade, musamman Naira 50, 100 da 200, sun yi karancin da wani lokacin dole a fasa ciniki idan ya kama sai an bayar da canji.”
“Sannan ko shakka babu wannan babban kalubale ne ga talaka mai karamin karfi, sannan kuma ga halin matsin rayuwa da ake ciki; yanzu da wane talaka zai ji?” Ta yi tambaya.
Wakilinmu ya zanta da Abba A. Ali, matashi mai hada-hadar POS a bakin babbar tashar Damaturu, inda ya bayyana cewa haka batun yake, “gaskiya a ‘yan kwanakin nan muna fuskantar matsalolin karancin takardun kudade, wanda abin ya kai ga sai ta hannun ‘yan kasuwa muke zuwa neman takardun kudaden, sannan mu zo mu kasa a wajen da muke gudanar da harkokinmu.”
“Sannan babbar damuwar ita ce, ba ma samun takardun kudaden a hannun bankuna, saboda kullum abin da suke gaya mana shi ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ba ya ba su isasshen takardun kudaden wanda za su bai wa abokanan huldarsu.”
Haka zancen yake a can Maidugurin jihar Borno, yayin da a zantawarmu da malama Fatima Mustafa, ta shaida cewa sun daina zuwa bankuna neman kudi, saboda kullum zancen daya ne babu isasshen takardun kudaden.
“Wanda saboda haka ne ma ya sanya sai dai mu je wajen masu POS, a wajen ne kadai za a iya samun takardun kudin, shi ma bai taka kara ya karya ba.”
Fatima Mustafa ta kara da cewa, sakamakon haka ya jawo talakawa na fuskantar karin matsin rayuwa saboda yadda sau tari cinikayya idan ta hada da kananan takardun kudin na wahala ko kuma a fasa.
Abeokuta
A garin Abeokuta babban birnin JIhar Ogun sabon tsarin karbar kudin ya fara aiki in da aka takaita yawan kudin da abokan huldar bankuna za su iya karba a rana. Bayanai sun nuna cewa, masu POS ba za su iya karbar kudin da ya wuce N50,000 a rana ba, N250,000 ke nan a mako maimakon N500,000 a mako kafin wannan tsarin ya fara aiki.
Wannan yana kuma zuwa ne a daidai lokacin da aka kayyade wa musu ajiya a asusun bankuna karbar abin da wuce N40,000 a rana, haka kuma an lura da cewa, yawancin na’urar karbar kudi (ATM) kuma bas u aiki.
Bayanin da jaridar LEADERSHIP Hausa ta samu ya nuna cewa, sabon umarnin ya tsara cewa, mai cire kudi a na’urar ATM na bankinsa zai iya karbar Naira N40,000, yayin da wadanda ke son cire kudi a ATM da ba bankinsa ba aka kayyade masa N20,000.
Ya zuwa yanzu wannan umarnin na kawo cikas ga masu harkar sana’ar POS, shi ya sa wasu daga cikin masu sana’ar suka nemi Babban Bankin Nijeriya CBN ya kawo musu dauki musamman ganin yadda abin ke kawo tarnaki ga harkokinsu na yau da kullum.