Bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, Amurka ta yi gwagwarmayar tabbatar da ‘yancin kasuwanci a duniya wajen kafa tsare-tsare da suka kunshi bangarori daban-daban ta hanyar Babbar Yarjejeniyar Haraji da Cinikayya ta GATT, har daga bisani aka samar da Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO). To, sai dai kuma, matakan da ta dauka kwanan nan na kare-karen haraji da dabarun kariyar cinikayya sun zama abin kunya, tare da bata rawarta da tsalle.
Mummunan tasirin matakan nata ba kawai ya tsaya ga karin haraji ba ne kadai, nema take ko ta halin kaka sai ta mamaye batun ci gaban fasaha a duniya. Tun daga zuwan Trump a farkon shekarar nan, kasar ta ci gaba da aiwatar da tsauraran matakan kariyar fasaha, da dankwafar da kasashe masu tasowa da karin matsin lamba ga manyan kasashe.
- Gwamnatin Kano Ta Fidda Sabbin Dokoki Domin Yaƙi Da Gurɓata Muhalli
- Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman Zamani: Jigawa Ta Baje Kolin Aikin Noma A Abuja
Kasar Sin ta sha daukar matakai don mayar da martani ga Amurka, haka nan sauran kasashe masu kumbar susa, amma kasashenmu na Afirka, musamman ma wadanda suka fi dogaro da kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasuwannin Amurka, me za su yi?
Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma.
Nijeriya da Afirka ta Kudu da suka fi karfin tattalin arziki a yankin, Amurka ta kakaba musu haraji na kaso 14% da 30% bi-da-bi, saboda rashin imani kuma karamar kasa kamar Lesotho wacce du-du-du karfin tattalin arzikinta na GDP bai wuce dala biliyan 2 ba, aka dankara mata karin harajin da kashi 50%.
Galibin tattalin arzikin kasashen Afirka ya fi dogaro ne da fitar da kayayyaki zuwa ketare don dorewar samar da aikin yi da kudaden shiga ga gwamnatoci, to amma kuma yanzu Amurka ta zama kadangaren bakin tulu. Babu makawa kasashen Afirka su kara karkata zuwa kasar Sin da sauran kasuwanni don samun damammakin cinikayya. Kamar yadda Shugaban Ghana John Mahama ya bayyana kwanan baya, wadannan sauye-sauye da ake samu kwanan nan na iya zama alheri ga Afirka ta hanyar dogaro da kansu.
Kasashen Afirka za su iya amfani da yanayin da ake ciki wajen zurfafa alaka da Sin, wadda ta kara habaka kasuwancinta da zuba jari a duk fadin nahiyar. A maimakon kari, ita kasar Sin ta bullo da manufar cire harajin ne ma ga kasashen Afirka 33 da suka fi fama da koma bayan tattalin arziki, da ba da damar shiga kasuwanninta. Wannan ya bude sabbin damammakin ga masana’antun Afirka su fitar da kayayyakinsu zuwa kasar musamman a fannin noma.
Haka nan, kasashen Afirka za su iya yin hadin gwiwa da kasar Sin don inganta kasuwancinsu a bangaren fasahohin zamani wadda duniya ke kara karkata a kai, inda hakan zai karfafa samar da tsarin cinikayya ta intanet da bude sabbin kasuwanni masu amfani da fasaha.
Da yake yawancin kasashen Afirka sun riga sun karbi shawarar ziri daya da hanya daya na BRI, wanda ke samar da kudade don ayyukan more rayuwa, za su iya amfani da wannan ma don kara karfafa hada-hadar sufuri da kyautata huldar cinikayya da za su kara musu kwarin gogayya da sauran shiyyoyin duniya. Bugu da kari, gwamnatocin Afirka na iya karfafa ‘yan kasuwa na gida su shiga cikin hadin gwiwar da suke kullawa da Sin don karfafa masana’antu na cikin gida.
Tabbas, ta hanyar yin cudanya da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni masu dacewa, kasashen Afirka za su iya rage illar kare-karen harajin Amurka, da samar da daidaiton huldar cinikayya mai tallafa wa ci gaban tattalin arzikinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp