Wasan da aka buga a daren ranar Litinin tsakanin kasar Belgium da Sweden, an dakatar da shi a minti na 40 da fara wa bayan samun rahoton harbe wasu mutum biyu har lahira a Brussels.
Firaministan Belgium, Alexender De Croo ne ya bukaci hakan bayan da aka samu rahoton kisan wasu magoya bayan kasar Sweden su biyu a Brussels babban birnin kasar ta Belgium.
Hukumar kwallon kafar Turai, UEFA ta rubuta a shafinta na X cewar, bayan shawarwari da ta yi, ta dauki matakin dakatar da wasan tsakanin Belgium da Sweden har sai zuwa wani lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp