…CI GABA DAGA MAKON DA YA GABATA
Alamomi masu nuni zuwa kamuwar cutar al’aurar mace ya danganta da irin ciwon da abin da ya jawo shi.
Kadan daga ciki: Zafi yayin fitsari, ciwo daga wajen al’aurarta, canzawar gaba ba kamar yadda ta saba gani ba, zafi yayin saduwa da miji.
yadda za ku hada sabulun ko ku saya
Abubuwan da za ku tanada:
Bagaruwa (Za ku samu a wajen masu magani gargajiya ), sabulun Zaitun ( Za ku samu a shagon maganin Musulunci, farin miski, Hulba na ruwa. Amma zaplan Zaitun ake hadawa da shi ki duba idan za ki saya amma idan kin rasa zaflan za ki iya sanyan Zaitun.
Yadda zaku hada:
In kin sayo sai ki dauki bagaruwa ki daka ta yi laushi ki zuba a roba, sai ki yayyanka sabulun Zaitun din kanana a kan garin bagaruwa ki nemo miski ki hada tare ki kwaba shi da ruwan Hulba, ki kwaba sosai ya yi kauri ya damku, sai ki zuba a roba mai kyau ki rufe.
Idan kwabawa zai baki wahala ki daka a turmi, in kin gama wanka sai ki wanke gabanki da shi. Idan kika kiyaye wadannan babu wani abin da zai hana farjinki dandano ko ni’ima, kuma babu ruwan ki da wani matsi idan za ki yi aure haka za ki shiga gidanki kuma za ki ga yadda za ki gigita mijinki ba tare da kin saka komai a gabanki ba.
Gyaran gaba bayan Haihuwa:
Ina matan da su kai haihuwa da yawa ko kuma Mata masu matsalar budewa, dole duk macen da ta haihu ta gyara kanta don ita mace ‘yar gyara ce, mu hankalta mata a farka.
Abubuwan da za ku tanada:
Alobera, Karo, Zaitun, Kanunfari.
Ku samu Alobera da Karo ku jefa kanunfari, ku tafasa ku dinga kama ruwa da shi. Sannan idan kika samu ganyen Alobera ki matse ruwan ya fito ki dinga wanke gabanki, wanke wa da ruwan dumi, sai kuma ki dinga shafa Zaitun in za ki wurin maigida
A na kiran su Micro–organism da Turanci. Ku sani cewa shi farji da a ke magana a kan cututtukansa shi ne wanda Allah ya halitta da wani sinadari na mayen karfe da wata tsoka kuma tana da baki guda biyu hagu da dama. Yayin da sha’awar mace ta motsa sai ta rika motsi dai-dai kuma tana iya yin rauni har ta daina motsi.
Wannan tsoka kamar fulogi ne a jikin babur, yayin da ta yi ma ta yawa, sai ta kasa motsi, daga nan sai sha’awar ‘ya mace ta dauke, domin ita wannan tsoka ita ce ke feso wani ruwa wanda shi ke sauko da wani ruwa da yake da jin dadin mu’amalar jima’i kuma yake sa wani zaki tsakanin mace da miji.
Idan daya daga ma’aurata ya samu matsala, sai ka ga auren ya ki zaman lafiya. Amma idan babu matsala sai ka ga a na zaune lafiya cikin shauki da annashuwa.
Mafi yawa mata masu ciki su na kamuwa da cututtuka daga wasu kwayoyin halitta da ke rike al’aurar mata, saboda gabansu ba ya rabuwa da danshi. Wadannan kwayoyin halittu su ne, bacteria, fungi da sauransu.
Alamomi masu nuni izuwa kamuwar cutar al’aurar mace ya danganta da irin ciwon da abin da ya jawo shi.