• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Man Bilicin Ke Yi Wa Fatar Mutum Illa

by Sani Anwar and Sulaiman
4 months ago
Man Bilicin

Shafa man bilicin don kara haske ko farin fata, abu ne da za a iya cewa; ya zama ruwan dare, musamman ga ‘yan Afirka ko bakar fata.

Wasu da dama suna amfani da man ne da niyyar fatarsu ta yi haske ko fari, yayin da wasu kuma ke amfani da shi cikin rashin sani, musamman yadda da yawan mutane ba su damu da sinadaran da ke cikin man da suke amfani ko shafawa ba.

  • An Daure ‘Yan Nijeriya Uku Shekaru 15 A Bisa Laifin Zamba A Indiya
  • Wang Yi Ya Nanata Matsayin Taiwan Yayin Tattaunawa Da Takwaransa Na Faransa

Man bilicin, yana aiki ne a fata wajen rage samar da tawadar rinin fata, wato ‘melanin’ da yaren likitanci. Tawadar rinin fata, ita ce ke samar da launin fatar mutum. Sannan kuma, wannan tawada ce ke kare fatar mutum daga kaifin hasken ‘ultrabiolet radiation’, wanda ke zuwa cikin hasken rana, wanda wannan haske ne mai hadari da ke iya haddasa kansa ko dajin fata.

Har ila yau, ana amfani da man bilicin, domin haska ko kodar da wani kebabbin sashin jiki kamar; nankarwa, bakin tabo, digon baki, tabbura-tabbura (tawadar Allah) da saura makamatansu, domin sajewa da jiki. Sai dai, wasu kuma suna amfani da man bilicin din ne, domin sauya launin fatarsu baki-daya.

Likitoci da sauran masana kiwon lafiya, suna ta jan hankalin mutane, domin su gane hadarin amfani da man bilicin, tsawon lokaci. Hadarin yana zuwa ne, sakamakon wasu muggan sinadarai da ke kunshe cikin man bilicin din. Kazalika, wadannan sinadarai, na yin mummunan lahani ga sassan jiki daban-daban.

LABARAI MASU NASABA

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

 

Daga cikin sinadaran akwai:

‘Hydrokuinone, corticosteroids/hydrocortisone, Mercury’ ko kuma sunaye kamar haka: ‘calomel, mercuric, mercurous, ko mercurio’.

Idan mutum ya duba takardar da ke like a jikin mazubin man da ya siya, domin ganin bayanan sinadaran da ya kunsa, zai ga wadannan a jiki.

A kula, kada a sake a zabi duk wani man shafawar da ke dauke da daya daga cikin sinadaran da aka ambata a sama.

Daga cikin haduran amfani da wadannan sinadarai sun hada da:

1- Kodewar fata tare da bayyanar launin shudi-shudi ko kore-kore a fata.

2. Saurin tsufa ko yanƙwanewar fata.

3. Sirancewar fata, wato kaurin fata zai rika raguwa sannu a hankali.

4. Bayyanar jijiyoyin jini a kasan fata, wadanda da ba a iya ganin su.

5- Haifar da cutar Kansa ko dajin fata.

6- Tabin kwakwalwa ko tabin hankali kai tsaye.

7- Ciwon Koda: ‘Mercury’, mugun sinadari ne da ya yi kaurin suna wajen haddasa ciwon koda, saboda yadda yake lalata jijiyoyin jinin kodar baki-daya.

8- Ciwon hanta da matsalar jijiyoyin laka baki-daya.

9- Haifar jarirai masu tawaya, idan an yi amfani da man bilicin yayin goyon ciki.

Tuni hukumomi a Kasashen Ingila da Amurka suka haramta siyar da man shafawa da ke dauke da irin wadannan sinadarai, saboda hadarin da suke da shi ga lafiya. Sai dai, har yanzu, kasuwar ire-iren wadannan mayuka na ci gaba da ci a sauran kasashen duniya duk kuwa da kwarmata hadarinsu ga lafiyar da ake yi.

Idan kana ko kina da sha’awar amfani da man bilicin ko kuma damuwa game da yanayin fatarka ko fatarkiki, tuntubi likitan fata kafin fara amfani da duk wani irin nau’in man bilicin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
Kiwon Lafiya

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

October 11, 2025
Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?
Kiwon Lafiya

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

October 5, 2025
Matsalar Tasgadewar Kashin Baya
Kiwon Lafiya

Matsalar Tasgadewar Kashin Baya

September 27, 2025
Next Post
Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki

Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.