Bisa lura da irin manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin yaki da fatara da kyautata yanayin zaman rayuwar alummun Sinawa, wannan batu yayi matukar jan hankalin duniya duba da girman alkaluman miliyoyin mutanen da kasar Sin ta tsame daga kangin talauci.
Hakika, masana na ganin cewa kasar Sin tana dora muhimmanci kan batun ayyukan kawar da talauci a cikin yankunan karkara, kuma ta cimma muradun neman ci gaba mai dorewa na MDD ta hanyar amfani da aikin gona na zamani, wannan a cewarsu, wata fasaha ce mai kyau da za ta taimakawa sauran kasashe masu tasowa da ma duniya baki daya.
Idan zamu iya tunawa, a kwanakin baya ne aka shirya wani taro a birnin Qujing dake lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin, domin bitar irin nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin kawar da talauci da raya yankunan karkara.
A yayin taron, an jiyo mataimakin firaministan kasar Sin, Hu Chunhua, ya yi kira da a kara kokarin karfafa nasarorin da aka cimma na yaki da talauci da tabbatar da aiwatar da manufofin da aka tsara na farfado da yankunan karkara domin samun moriya mai dorewa.
Wannan batu dai zamu iya cewa, zai jima a zukatan masu fashin baki da sharhi kan al’amurran zamantakewar rayuwar bil adama na kasa da kasa. Batun dai ya sa masanan kasa da kasa ke cigaba da bayyana ra’ayoyinsu game da wannan babban tagomashi da Sin ta samu.
A kwanan nan, wani kwararren masani a Najeriya yace, nasarorin da kasar Sin ta cimma a yaki da fatara ta samar da wani muhimmin darasi da ya kamata kasashe maso tasowa su koya domin tsame dunbun al’ummunsu daga cikin yanayin kangin talauci a cikin kayyedadden lokaci.
A wata hirar da ya yi kwanan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, babban birnin Najeriya, dakta Sheriff Ghali Ibrahim, shugaban sashen nazarin kimiyyar siyasa da huldar kasa da kasa na jami’ar Abuja, ya ce kasar Sin, a kokarinta na tsame sama da mutane miliyan 800 daga kangin fatara a cikin wasu ‘yan shekaru, ta yi amfani da dabaru na zahiri, kuma ta gwadawa duniya cewa ita jagora ce. Don haka, ya kamata kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika, da na Latin Amurka, da na Caribbean, su yi koyi da kasar Sin a shirinta na yaki da fatara.
A tsokacin da masanin ya yi ya ce, hangen nesan da kasar Sin ta yi, ya taka muhimmiyar rawa a shirinta na yaki da talauci, inda ya bukaci kasashe masu tasowa dake da dunbun albarkatun kasa, da su yi amfani da su wajen tsara dabarun yadda za su tinkari yaki da fatara a kasashensu.
Ko shakka babu, kasar Sin tana iyakar kokarinta wajen sauke nauyin alummarta, a hannu guda kuma, tana bada gagarumar gudunmawa ga cigaban kasa da kasa. Masana da dama sun bayyana kasar Sin a matsayin kasar da ta fi bada gudunmawa ga ci gaba mai dorewa a Afrika haka kuma babbar mai taimakawa kasashe masu tasowa.
Babban abinda ake fata dai shine, kasashen masu tasowa su yi koyi salo da kuma irin dabarun da Sin ke amfani dasu wajen tsamewa alummarta kitse daga wuta, dama masu hikimar magana na cewa, “daga na gaba ake gane zurfin ruwa.”