Wani abun takaici ya nuna yadda wani matashi ɗan shekara 35 a duniya a jihar Bauchi, Tijjani Ahmadu Diye, ya kama matarsa da dukan tsiya har ma ya yi yunƙurin kasheta da tabarya kawai domin ya samu damar sace mata ‘talabijin’.
Yadda lamarin ya faru kuwa, a ranar 2 ga watan Disamba, ya fito cikin gidansu ya yi ta yekuwar cewa ‘yan fashi da makami sun shigo cikin gidan domin juya tunanin matarsa.
- Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Masu Maulidi A Kaduna
- Da Ɗumi-Ɗumi: Jam’iyyar APC Ta Kori Shugabanta Na Jihar Bauchi, Aliyu Misau
Ana hakan ya shiga cikin ɗaki ya umarci matarsa da ta lulluɓe fuskatar da ƙyalle, inda ya fita waje ya sake dawowa cikin ɗakin shi ma fuskarsa a rufe, nan take ya rufe matar tasa da dukan tsiya da ciki har da mari domin ya samu nasarar yin awun gaba da talabijin ɗinsu da zimmar sayarwa domin ƙara jari a shagonsa.
A wata sanarwa daga shalkwatar ‘yansandan jihar Bauchi ɗauke da sanya hannun CP Ahmad Muhammad Wakil ta yi ƙarin haske da cewa: “Cikin gaggawa bayan samun rahoton faruwar lamarin, jami’anmu sun dira wajen da abun ya faru inda suka ɗauki wacce aka jikkata zuwa asibitin kwararru da ke Bauchi inda a halin yanzu take amsar kulawar likitoci.”
“Bincike farko-farko ya nuna yadda wanda ake zargin ya amsa laifinsa ba tare da wani ɓata lokaci ba. A amsa laifin nasa, wanda ake zargin ya yi yekuwar ƙarya na cewa ‘yan fashi da makami sun shiga cikin gidansu.”
“Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewar niyyarsa shi ne ya kashe matarsa domin ya samu damar ɗaukan talabijin dinsu domin ya sayar ya samu kuɗin ƙara jari a shagonsa,” sanarwar ta ce.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya umarci a mayar da kes ɗin zuwa sashin binciken manya laifuka domin fadada bincike da gano haƙiƙanin abun da ya faru na cewa abun da mutumin ya faɗa haka ne ko akasinsa.
Sanarwar ta ce, bayan an kammala gudanar da bincike, za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya manta sabo domin fuskantar doka daidai da laifin da ya aikata.