A ranar Talata ne ‘yan tawayen Houthi suka bayyana ce wa su suka kai hari kan wani jirgin ruwan dakon mai na Norway da ke tafiya a tekun Rum zuwa Isra’ila.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Yahya Saree ya fitar, ya ce sun kai harin ne bayan da jirgin ruwan yaki bin gargadin da suka gindaya masa.
- MDD Za Ta Sake Shirya Taron Kada Kuri’a Kan Tsagaita Wuta A Gaza
- Kuri’ar Kin Amincewar Amurka Ta Tsagaita Wuta A Gaza Adawa Ce Ga Bukatar Bil’adama
A cewar Yahya, jiragen ruwa da yawa a cikin kwanaki biyun da suka gabata sun bi shawarwarin nasu na taka-tsantsan, inda suka tsira daga harin nasu.
Sai dai mai magana da yawun Houthi ya yi ikirarin cewa jirgin ruwan Norway ya yi watsi da sanarwar da suka yi, lamarin da ya sa suka dauki matakin ramuwar gayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp