Wata mota ta buge wani da ake zargin mai kwancen waya ne akan babbar titin gidan Zoo da ke cikin birnin Kano a daren Lahadi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.
- Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kafa Majalisar Dattawan Kano
- Shari’ar Kano: Kanawa Na Farin Ciki Kan Nasarar Abba A Kotun Koli
A cewar sa, motar ta buge barawon ne a lokacin da yake kokarin arcewa bayan ya kwace wayar daga hannun wata yarinya.
Ya ce wanda ake zargin ya yi amfani da Adda ne don tsoratar da yarinyar wajen kwace mata wayarta, yana tsakar gudu ne motar ta buge shi.
Kiyawa ya ce, jama’a ne suka kira jami’an ‘yansandan don kai barawon da aka buge ya suma zuwa asibiti.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kwacen waya ya yi kamari a cikin birnin Kano, musamman cikin dare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp