‘Yan Nijeriya dai sun dade suna kokawa kan samun sahihin zabe mai cike da adalci tun dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.
Tun daga lokacin da ake gudanar da ayyukan zabe ta hanyoyin da aka saba, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ci gaba da bullo da hanyoyin fasaha don inganta zabuka a Nijeriya.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane
Wadannan hanyoyi ba sa kasantuwa ba tare da kalubale ba, kuma lokaci ya yi da za a magance matsaloli ta hanyar fasahar sadarwa.
Yayin da kasar nan ta kusan shiga babban zaben 2023, an bullo da hanyar fasahar zamani da ake kira na’urar BBAS, domin yin amfani da ita a zabukan 2023.
Ga wasu daga cikin hanyoyin da na’urar BBAS ke gudanar da aiki kamar haka:
Tun a 1999, rajistar masu jefa kuri’a da tattance su da tattara sakamakon zabe da hannu aka yi.
Amma a shekarar 2016, rajistar masu jefa kuri’a da tantancewa da watsa sakamakon ya zama ta na’urori da suka hada da EBR, AFIS, SCR, inda har aka zo na’urar BBAS.
Hukumar INEC ta gabatar da na’urar BBAS ne domin tabbatar da sahihin zabe a Nijeriya.
Duk da cewa wannan na’ura ta dade ana amfani da ita, an fara gwada ta ne a zaben cike gurbi na mazabar Isoko ta Kudu a Jihar Delta a ranar 10 ga Satumbar 2021.
Daga baya aka yi amfani da na’urar a zaben gwamnan Jihar Anambra a ranar 6 ga Nuwambar 2021, kuma aka sake amfani da ita a zabukan gwamnonin Ekiti da Osun.
Duk da irin damuwar da ‘yan siyasa suka nuna wajen amfani da na’urar BBAS, INEC ta bayyana cewa babu gudu babu ja da baya kan amfani da ita a zaben 2023.
An dai yi amfani da na’urar BBAS ne wajen tattance masu kada kuri’a da saka sakamakon zabe a shafin hukumar INEC ta yadda za a samu sahihin zabe a 2023.
Na’urar BBAS tana daukar bayanan rumfar zabe, jimillar wadanda suka yi rajista da kuma yawan adadin wadanda suka yi zabe.
Baya wadannan ayyuka, za a kuma yi amfani da BBAS wajen mika hoton sakamakon zabe a rumfunan zabe zuwa shafin hukumar INEC a yadda jama’a za su gani, muddin sun shiga shafin hukumar zabe.
Daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta a harkar zabe shi ne, kura-kuran da ake tabkawa a tsakanin rumfunan zabe da cibiyoyin tattara sakamakon zabe. A wasu lokuta, ana sace sakamakon zabe ko a canza ko ma a lalata.
Wannan ya sa hukumar INEC ta yi tunanin yin amfani da na’urar BBAS wajen watsa sakamakon zabe kai-tsaye tun daga rumfunan zabe zuwa shafin INEC.
Wannan tsarin ya rage kura-kuren da mutum yake tabkawa da jinkirin tattara sakamakon zabe. Haka nan yana habaka samun sahihin bayanai wajen tattara sakamakon zabe.
Don haka, wannan ya nuna cewa dole ne a fara tantance katin jefa kuri’a da BBAS domin tabbatar da cancantar mutum kafin ya sami damar kada kuri’a a ranar zabe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa na’urar BBAS tana aiki ne a layi daya kuma ba ta dogara da intanet wajen tattance masu kada kuri’a a ranar zabe.
Shugaban INEC ya shaida wa BBC cewa yana bukatar hanyar sadarwa ne kawai don watsa sakamakon zabe.
Hukumar INEC ta jaddada cewa za a yi amfani da na’urar BBAS a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
An samu cikas da na’urar BBAS a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, lamarin da ya kai ga sukar hukumar zabe da kin amincewa da sakamakon da jam’iyyun adawa suka yi.
Da yake magana a Abuja, shugaban hukumar INEC, Yakubu Mahmood, ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta a lokacin zaben shugaban kasa da na’urar BBAS za a yi amfani da ita a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi domin tantance masu zabe da tura sakamakon zabe a shafin INEC.
Ya ce: “Na’urar BBAS ya yi nisa wajen tsaftacewa da tantance masu kada kuri’a kamar yadda ake iya gani daga sakamakon zaben da aka yi kwanan nan. Tun a makon da ya gabata, hukumar ta kara yin nazari kan na’urar don tabbatar da cewa an kauce wa kura-kurai da aka samu a baya, musamman wajen shigar da sakamakon zabe. Muna da tabbacin cewa ci gaba da amfani da na’urar zai yi aiki da kyau.
“Har ila yau, hukumar yaba da hakuri da fahimtar da ‘yan Nijeriya suka yi mata. Ba mu dauki wannan a wasa ba. Haka nan muna godiya da kishin kasa na shugabannin siyasa da na gargajiya da na addini da na al’umma da suka nemi a kwantar da hankula lokacin gudanar da zabuka.
“Haka kuma, hukumar ta yaba da rawar da masu sa ido kan zabe ke takawa, wadanda wasunsu har yanzu suna kasar. Muna kira a garesu su kara hazaka wajen saka ido a sauran zabukan da Nijeriya za ta gudanar, domin sun kasance wani muhimmin bangare na babban zaben da aka ba su izini har su saka ido a kansa, saboda suna da matukar muhimmanci a duk lokacin da ake gudanar da zabe a Nijeriya.
“Saboda haka, hukumar ta yaba wa duk masu sa ido na cikin gida saboda rahotannin da suka bayar wanda zai taimaka mana matuka yayin da muke kammala babban zaben 2023. Muna sa ran samun cikakkun rahotannin da za su taimaka mana.
Shugaban hukuman INEC ya ce hukumar za ta yi aiki tukuru domin shawo kan kalubalen da aka fuskanta a zaben da ya gabata.
Ya ce za a gudanar da horaswar na wartsakewa ga ma’aikatan wucin-gadi domin kwarewa ga aikin da hukumar take yi.
Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke zamanta a Abuja, ta bai wa hukumar INEC izinin sake fasalin na’urar BBAS wajen amfani da ita a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi domin tantance masu kada kuri’a da tura sakamakon zabe a shafin hukumar INEC da ta yi amfani da shi wajen zaben shugaban kasa.
A wani mataki na bai-daya da wasu alkalai uku suka yanke, kotun ta ce dakatar da hukumar zabe daga sake fasalin BBAS zai yi illa ga zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da aka yi ranar Asabar da ta gabata.
Ta yi watsi da korafin da jam’iyyar LP da dan takararta na shugaban kasa, Mista Peter Obi suka shigar kan matakin na INEC na sake fasalin daidaita dukkan na’urar BBAS.
A cewar kotun, bayar da izinin da Obi da jam’iyyarsa suka nema zai bayar da hannun agogo baya ga hukumar INEC.
Bayan haka, ta kuma bayyana cewa INEC a cikin takardar karar da ta shigar a gaban kotu, ta ba da tabbacin cewa ba za a iya takurawa ko a bata bayanan da ke kunshe cikin BBAS ba, domin za a adana su cikin sauki daga wata na’ura ta musamman ta yadda a duk lokacin da ake bukatan bayanai za a samu ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma kara da cewa, Obi ko LP ba su yi sabani a kan abubuwan da aka rubuta a cikin takardar shaidar karar INEC ba, tun da ba a kalubalanci irin wadannan abubuwan ba, dole ne a yi watsi da karar.
Sai dai kotun ta umurci INEC da ta bai wa wadanda suka nema damar bincika tare da gudanar da gwajin na’urar tantance duk kayan zabe da aka yi amfani da su wajen zaben, tare da ba su sakamakon binciken da aka yi na zahiri game da na’urar BBAS.
Kwamitin da Mai Shari’a Joseph Ikyegh ya jagoranta ya caccaki Obi da LP kan maimaita bukatar su na a bar su su duba tare da yin kwafin kayan zaben da ke hannun INEC.
Ganin cewa an amince da bukatar tun da farko, kwamitin ya ce maimaita rokon tamkar cin zarafin kotu ne.
Idan dai za a iya tunawa INEC ta dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalusun jihohi saboda ta samu damar kara seta na’urar BBAS tun da kotu ta umurci ta yi amfani da shi wajen bayyana sakamakon zabe.
Ta ci gaba da cewa, idan ba dan umurnin da kotu ta bayar a baya ga Obi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, musamman ma abin da ya hana ta sake saita na’urar BBAS, zai yi wahala ta iya gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da wannan na’ura, saboda kunshe suke da bayanan na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
Obi da jam’iyyarsa sun shigar da kara mai dauke da lamba kamar haka: CA/PEC/09m/23, ida suke nemi a ba su izinin gudanar da binciken cikin na’urar BBAS da aka yi amfani da su wajen zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
Masu shigar da kara ta hanyar tawagar lauyoyinsu karkashin jagorancin Dakta Onyechi Ikpeazu sun ce muhimmancin neman wannan bukatar tasu shi ne, domin fitar da bayanan da ke cikin na’urar BBAS da ke kunshe da ainihin sakamakon zabe tun daga rumfunan zabe.
Sun nemi a bar su don gudanar da binciken zahiri kan na’urar BBAS da sauran kayayyakin zabe da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya tare da yin kofin duk bayanan da ke cikin BBAS.
Yayin da take adawa da bukatar, INEC ta shaida wa kotun cewa akwai jimillar BBAS 176,000 da aka tura rumfunan zabe a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
“Kowace rumfar zabe na da nata na’urar BBAS da muke bukata mu yi amfani da ita a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a zabe mai zuwa.
“Zai yi mana matukar wahala a cikin wannan lokaci mu sake fasalin BBAS guda 176,000.
“Mun rigaya mun bayyana a cikin takardar shaidar kara cewa babu wani bayani a cikin BBAS da zai a iya rasawa a lokacin da mu tura duk bayanan da ke cikin BBAS zuwa babban kundin ajiye bayananmu.
“Muna bukatar daidaita BBAS. Don haka, bayar da wannan bukata za ta iya kawo jinkiri wajen gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi,” in ji babban lauyan INEC, Tanimu Inuwa (SAN).
Dole dai daga baya INEC ta dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da mako guda, domin samun damar saita na’urar BBAS.
Sai dai kuma sakamakon wannan takaddamar ya sa hukumar INEC ta dora wasu sakamakon zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a shafinta.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa jam’iyyun adawa da wasu ‘yan Nijeriya sun caccaki INEC kan gazawarta wajen saka sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya nan take a shafinta, ta yadda kowa zai ga sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya nan take.
Ko da yake hukumar ta yi bayanin cewa matsalar sadarwa ta kawo cikas wajen yada sakamakon zabe shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, wanda da yawa masu suka suka ki yarda da shi.
Sai dai kuma, INEC ta ce ta yi nasarar gyara wannan kuskure, inda ta ce kowa ya ga yadda ta wallafa sakamakon zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi kai-tsaye.
Binciken da wakilinmu ya yi a ranar Asabar ya nuna cewa a Jihar Ogun an gabatar da sakamakon zabe guda biyu; Jihar Filato, an gabatar da sakamako 12, Jihar Zamfara, an gabatar da sakamako 11, Jihar Ribas dai an gabatar da sakamako 80, a Jihar Legas kuma guda 85.
Lallai masu sharhin al’amurar shiyasa sun tabbatar da cewa yin amfani da na’urar BBAS wajen bayyana sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi ya yi matukar rage magudin zabe.
A cewarsu, amfani da BBAS ya sa wasu gwamnoni da ke kan garagar mulki suka sha kaye, yayin da wasu kuma suka sami nasara dakyar.