Idan aka yi buris, ta hanyar kin kula da rauni, miki ko gyambo a wani sashe na jiki; ba tare da bin hanyar magance shi ba, hakan zai iya jawo shigar kwayoyin cutar bakteriya ko fungai cikin wannan rauni.
Da zarar wadannan kwayoyin cututtuka sun shiga rauni, daga nan ne kuma sai raunin ya zama gyambo. Sannan, kamar yadda aka sani ne; alamomin gyambo sun hada da kumburi, ciwo, dumi, sauyin launin fata, lalacewar tsoka, taruwar mugunyar ruwa ko jinni ko kuma diwa.
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji A Kan Fasahar Sadarwa
- ‘Yan Nijeriya Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Karin Kudin Kiran Waya
Har ila yau, idan gyambo na kusa da gaba; yana iya jawo rikewar gaba da kuma wahalar motsa ta, sai dai da kyar ko da ‘yan dabaru.
Idan kuwa har aka yi buris da gyambon, kwayoyin cututtuka babu wuya za su kutsa cikin wannan gyambo; har su kai ga kama kashi da bargon kashin baki-daya cikin kankanin lokaci.
Haka zalika, a yayin da kwayoyin cututtuka suka kama kashi da bargo, lamari ne da babu wani bata lokaci da ke bukatar kulawa ta musamman, domin kuwa a wannan lokaci lamarin ya canza kai tsaye zuwa cutar kashi, (Osteomyelitis) a turance.
Don haka, ‘Osteomyelitis’; cutar kashi ce wadda idan ba a yi kokarin shawo kanta da wuri ba, na barazanar rage ingancin kashi ko lalata shi ma baki-daya. Kazalika, idan cutar ta tsananta; tana iya cinye kashin wannan sashen gaba kwata-kwata.
Bugu da kari, bayan cutar kashi da gyambo; haka nan wadanda aka yi wa tiyatar kashi su ma suna iya gamuwa ko samun wannan cuta ta kashi, idan aka samu akasi wajen shigar wadannan kwayoyin cututtuka; yayin ko bayan aiwatar da tiyata.
Saboda haka, da zarar mutum ya yi rauni ko ya samu miki; akwai bukatar gaggawar tuntubar likita, domin samun kulawarsa don guje wa afkawar wadannan kwayoyin cututtuka da kuma kiyaye wannan cuta ta kashi.