Ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Litinin ya jawo mummunan ambaliyar ruwan da ya ruguja Gadar Katarko a karamar hukumar Gujba a Jihar Yobe, wadda ta hada jihar da jihohin Borno da Gombe, mai tazarar kilomita 22 daga Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Zabtarewar gadar ya kawo cikas ga ma’aikatan hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA), a kokarin kai wa jama’ar da ambaliyar ruwan ta shafa a kauyen Mutai a yankin, wanda suka gamu da mummunan ambaliyar ruwan da ya shafe garin baki daya.
A wata sanarwar da shugaban hukumar YOSEMA, Dakta Mohammed Goje ya fitar ya tabbatar da ambaliyar ruwan tare da bayyana cewa gadar Katarko ta ruguje gaba daya sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da ya malala zuwa yankin.
Dakta Goje ya ce, “Wannan ita ce gada kuma titin daya tilo da ta hada Damaturu zuwa Gujba, Gulani da kananan hukumomin Biu.
“Haka kuma wannan ambaliyar ruwa ya shafi al’ummar Mutai, Buni Yadi da Gulani wanda katsewar gadar zai kara kawo damuwa ga jama’a, musamman a kauyen Mutai.
“Hukumar YOSEMA ta tuntubi sojoji domin samar da mafita ga al’ummar Katarko saboda yadda wasu jama’a ke yin dafifi a wurin don guje wa asarar rayuka.
“A hannu guda kuma, wannan na iya shafar tallafin gaggawa da muke kai wa jama’ar don ceton rayuwar al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa, sannan kuma Gwamnatin Jihar Yobe tana kokarin lalabo mafita wanda za ta taimaka wa wadanda ibtila’in ya rutsa da su,” in ji Dakta Goje.