Yayin da duniya ke fatan fita daga kangin talauci da ke barazana ga dorewar zaman lafiya, amma abin takaici, maimakon babbar yaya (Amurka) ta tallafa wa fatan, sai ga shi ita ke shirin jefa harkokin kasuwancin duniya cikin rudani.
Tun farkon da aka rantsar da sabon shugaban Amurka, Donald Trump ke fito da wasu tsare-tsare da sauye-sauye da ke barazana ga makomar kasuwanci a kasuwannin duniya.
Kasa kamar Amurka mai fadin kasuwa a duniya ta balle daga amintaccen tsarin kasuwanci na duniya, wannan hali ne na son kai na kasar da ya bayyana a fili, kuma hakan ka iya yin barazana ga tattalin arzikin kasashen duniya, ta hanyar gurgunta muhimmin tsarin kasuwancin.
A cewar Chad Bown, fitaccen masani a Cibiyar Tattalin Arzikin Duniya ta Peterson, “yunkurin da Amurka ke yi na kara harajin kwastam kan wasu kasashe, zai yi mummunar illa ga tsarin kasuwancin kasa da kasa. Ta hanyar nuna wariya a tsakanin abokan ciniki da zabga haraji ba tare da bin wata ka’ida ba, Amurka ta keta ka’idojin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya”.
Hanyar da Trump ya bi, tana tattare da kalubalen rarrabuwar kawuna a fannin kasuwanci, inda sabani zai maye gurbin kyakkyawar yarjejeniyar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashe biyu.
Karin harajin kwastam na iya haifar da yakin kasuwanci. Kasashen da wannan harajin ya shafa za su iya mayar da martani, lamarin da ka iya haifar da rudanin da zai cutar da kasuwancin duniya. Wannan na iya haifar da karin farashin kayayyaki, sallamar ma’aikata daga aikinsu, dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da takaita ci gaban tattalin arziki a duniya.
Don haka, ana kyautata tsammanin cewa, wannan sabon tsarin harajin zai sake fasalin yanayin kasuwanci a duniya, ganin cewa, wasu masana’antu za su fuskanci tsadar kayayyaki da kuma durkushewar hanyoyin samar da kayayyaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp